Muktar Anwar" />

Hanyoyin Gyara Sana’ar ‘Yan Keke Napep

Wasu daga cikin masu hayar baburan da na zanta da su, cikinsu akwai wani mazaunin unguwar Sabuwar Kofar Kabuga, Gwale, Kano, da ake kira da Lukuman Mai-wali, ya yi kuka da jami’an hanya da gwamnati ke turowa  don kula da ababen hawa. Lukuman, ya koka ne da jami’an Hukumar Karota na Kano, inda suke muzgunawar masu sana’ar baburan na A Daidaita Sahu dare da rana. Ya kara da cewa, yayinda Danjar Titi ta ba-da-hannu (yayinda ta nuna kore), sai ya zamana ababen hawan na ta wucewa, danjar na kokarin tsaida su (lokacin da ta nuna kala shigen dorawa, gabanin nuna jar danja), kana kokarin wucewa sai su kamaka, su ce ka karya doka, alhali, ba jar danja ce ba ta tsaida ka.

Akwai koke-koke iri-iri masu tarin yawa, da su ma masu hayar baburan; da masu hawa baburan,m; da masu siyen baburan; uwa-uba, da ma HUKUMA, za a ji kowannensu na gabatarwa. Amma kowa ya gyara ya sani, haka ma batawa. A bangaren hukuma kuwa, babban kukan da take yi da masu hayar baburan shi ne, karairaya Dokokin Hanya da suke yi babu kakkautawa.

Hanyoyin Gyara Abin-bi Don Kara Tsaftace Harkar Baburan Na A Daidaita Sahu

Babu shakka, duk wata matsala da za a ga na faruwa tattare da kowane lamari, hakika kam akwai matakan gyara kyawawa, wadanda dabbaka su kan taimaka ainun, wajen samun sauki, ko ma kawar da wannan matsala kacokan.

Akwai cikin Masharhanta dake da tunanin cewa, yin la’akari da wadannan shawarwari da za a gabatar, za su matukar ciccida wannan harka ta Keke Napep ko A Daidaita Sahu, zuwa ga matakin nasara abin-bege cikin wannan Kasa. Ga shawarwarin kamar haka;

i- Yin Taza-da-tsifa Ga Masu Son Tsunduma Cikin Harkar

ii- Jami’an Hanya Na Gwamnati Su Sanya-idanu Wajen Ganin Masu Baburan Na Dabbaka Shimfidaddun Dokokin Hanya

iii- Samar Da Wani Kakkarfan Kwamiti Da Zai Tirsasa Bin Dokokin Hanya

ib- Samar Da Karin Kotunan Tafi-da-gidanka Don Hukunta Masu Kangara Ga Dokokin Hanyar

b- Samar Da Masu Kula Da Jami’an Hanyar Game Da Aikin Da A Ka Dora Musu

bi- Kange Kananan Yara Kutsa-kai Cikin Harkar Baburan

bii- Wajabta Shigo Da Nagartattun Babura Zuwa Cikin Kasa Ba Tarkace Ba

A takaicen takaitawa, wadancan shawarwari bakwai (7) na sama da aka lasafto, na daga manyan nasihohi da wasu jama’a masu hangen-nesa suka gabatar, don son ganin an ceto wannan harka mai matukar alfanu ga tattalin arzikin Kasa da Al’uma daga balbalcewa. Zai yi kyau a dauko su daya-bayan-daya, don kara fayyace hakikanin inda aka nufata da su.

i- Yin Taza-da-tsifa Ga Masu Son Tsunduma Cikin Harkar;

Taza-da-tsifa ga masu son tsunduma cikin harkar baburan na nufin, sanya-idanu ga masu shiga cikin harkar. A fitar da wani kyakkyawan shiri ko tsari, wanda a karkashinsa, za a rika kula da halaye gami tarbiyyar wadanda ke kutsawa cikin sabgar dare da rana.

A yau, kowa ne mutum, na iya afkawa cikin harkar da rana-tsaka ne, ba tare da sanin, shin, daga wace jiha ce ya zo? Koko Dan wannan jiha ne? Yaya halayensa suke?. Duka wadannan muhimman tambayoyi dake bukatar amsawa, ba a la’akari da su wajen tantance masu sana’ar ta A Daidaita Sahu.

Tunda Duniya ta yarda cewa, a kan sami Barayi da ‘Yan Ta’adda dake amfani da wadannan Babura, ke nan, anya babu matsala a bar cigaba da gudanar harkar kara-zube haka? Ta wace hanya ke nan za a bi, wajen tantance masu son antayawa cikin sana’ar?. Dole ne gwamnati, musamman ta Karamar Hukuma ta shigo cikin sha’anin tantancewar, tare da hada-hannu-da-karfe da Dagatai gami da masu Unguwanni.

Wajen tantancewar, ba ya ga sanin daga inda mutum ya fito da halayyarsa, neman ya gabatar da Katinsa na Dan-kasa ma na da gayar alfanu, duba da yanayin da ake ciki na tabarbarewar tsaro a Kasa. Wajibi ne ga mai sha’awar shiga sabgar, ya gabatar da akalla mutane biyu (2) kamilallu da za su tsaya masa.

Akwai abubuwa iri-iri abin la’akari, wadanda gwamnati za ta zauna da Mutane Masana Kwararru, a dube su, a fede su, domin samar da ka’idoji da sharudda masu kyawo, da za su taimaka zuwa ga samar da mutane nagartattu cikin wannan Sana’a ta A Daidaita Sahu.

Gaba ta biyu dake magana game da kyautata wannan muhimmiyar sana’a ita ce;

ii- Jami’an Hanya Na Gwamnati Su Sanya-idanu Sosai Wajen Ganin Masu Baburan Na Dabbaka Shimfidaddun Dokokin Hanya;

Cikin kowace jiha a Najeriya a yau, ba a rasa jami’an hanya dake kula da zirga-zirgar ababen hawa: kula da cikakkiyar lafiyarsu, tare da lura da irin yadda suke kiyaye dokokin hanya ko akasin haka.

Da yawan irin wadancan jami’an hanya da muke da su, sun fi mayar da hankali ne kacokan, wajen kula da manyan motoci na haya da na dakon kaya; kananan motoci kanana, na gida da bas-bas na haya. Jami’an, ba su faye kulawa da Baburan na A Daudaita ba, wajen ganin sun dabbaka dokokin hanya.

Dole ne a shiryawa irin wadancan jami’ai wata bita ta musamman game da yadda za su bullowa da irin wadancan Kekuna na Napep, wajen ganin sun dawo bisa tafarkin bin dokokin da aka gindayawa ababen hawa. Sannan, wadancan jami’ai, kada su rika aiki cikin yanayi na zalunci ko urustawa masu baburan. Su ja su ne a jiki, su rika nusar da su muhimmancin bin dokokin.

Masu kunnen-kashi kuwa cikin masu sana’ar baburan, su fuskanci hukuncin da dokokin hanyar suka samar ga masu bijire musu.

Matakin gyara na kawo gyara na uku shi ne;

iii- Samar Da Wani Kakkarfan Kwamiti Da Zai Tirsasa Bin Dokokin Hanyar;

Ba ya ga ja a jiki, tare da nusar da masu baburan hayar da wadancan jami’ai ke yi dare da rana, akwai bukatar gwamnati na ta sake haife irin wannan Kwamiti na biyu, wanda zai rika aiki ne, ba-sani-ba-sabo.

Irin wannan kwamiti na biyu, a duk sa’adda ya fito bakin aiki, tirsasawa ce aikinsa. Tunda, masu baburan, jami’an farko, sun ja su a jiki, sun wayar musu da kai game da muhimmancin dabbaka dokokin hanya. Saboda haka, shi wannan kwamiti na biyu, kwamiti ne da bai da sassauci ko kadan, ga bara-gurbin dake karairaya dokokin hanyar bisa izgili da sake.

ib-Samar Da Karin Kotunan Tafi-da-gidanka Don Hukunta Masu Kangara Ga Dokokin Hanyar;

Samar da karin Kotunan, don hukunta masu kunnen-kashi cikin masu hayar Baburan, zai zamto tamkar wani abu wajibi, duba da dubban mutanen dake cure cikin sabgar hayar. Ta yadda zai zamto tamkar gamo-da-kasawa ne, kana balla dokar hanyar, sai hukunci ya dafe ka nan take.

Rashin samar da irin wadancan Kotuna na ga-wuri-ga-waina, zai haifar da cunkoso ne a Kotunan Shari’a da ake da su cikin Kasa. Ai yana daga dalilan kaucewa gosulo a kotuna ne, ake kafa Kotunan saurarar korafe-korafen Zabe, bayan kammala zabuka a Kasa: shi fa Zaben, daga wasu Shekaru zuwa wasu ne ake gabatar da shi, ballantana harkar babura da dubban daruruwan al’uma ke cikinta dare da rana.

b- Samar Da Masu Kula Da Jami’an Hanyar Game Da Aikin Da A Ka Dora Musu;

Cikin babbar sabga musamman wadda ta jibinci kula dubban rayukan al’uma irin wannan, bai kyautu kawai a wakilta wasu mutane hakkin tafiyar da ita, a dauke-kai ga barin su ba. Dole ne a samar da wasu mutane ta bayan-gida ko karara a zahiri, da za su rika sanya-na-mujiya bisa yadda ake tafikad da wannan babban aiki.

Mai karatu ya kwana da sanin cewa, ‘Yan Majalisu na Kasa da na Jihohi, na bibiyar irin yadda bangaren Zartarwa na Gwamnati ke tafiyar da ayyukan jama’a dake aze bisa wuyayensu. Kusan daukacin hukumomin gwamnati, za a iske cewa, akwai wasu a gefe dake bin-kwakkwafin irin yadda lamura ke gudana. Idan kuwa haka ne, wannan muhimmiyar sabgar dake lakume rayukan jama’a dare da rana, na daga manyan ababen dake kan gaba, wajen bukatar tantance yadda jami’ai ke mu’amalantar ta. Ko ba komai, hakan zai nuna an damu da kula da kare jinin al’umar da ake shugabanta.

[23:01, 09/10/2019] Mukhtar Anwar: Wadancan masu sanya-idanu ga jami’an hanyar, na da rawa abar yabo da za su iya takawa wajen inganta lamura cikin sha’anin masu baburan matuka gaya. Za su iya zama masu jan-kunnen jami’an, yayinda suka tasamma zalintar ko muzgunawa masu baburan hayar haka siddan ; ko suka yi yunkurin karbar cin-hanci daga gare su, yayinda suka karya wata doka cikin dokokin hanya ; ko neman shafa-musu-bakin-fenti ba da hakkinsu ba. Akwai dalilai tuli, wadanda za su nuna matukar muhimmancin bukatuwa zuwa ga samar da wannan Kwamiti na Sanya-idanu ga ayyukan Jami’an Gwamnati dake kula da kai-kawon ababen hawa musamman na hayar da a yau ake kira da Keke Napep ko A Daidaita Sahu.

bi- Kange Kananan Yara Kutsa-kai Cikin Harkar Baburan Barkatai;

Ba karamin abin takaici ne ba, ya zamana Yara kanana ‘yan kasa da Shekarun balaga, sun yawaita cikin masu tuka wadannan Babura na A Daidaita Sahu. Ko shakka babu, irin wadancan Yara, a halin Shekarunsu na yanzu, ya dace ne a ce suna kai-kawonsu tsakanin GIDA da MAKARANTA.

Cikinsu, babu ‘ya’yan Shugaban Kasa ko Minista; babu ‘ya’yan Gwamna ko Kwamishina; babu ‘ya’yan Ciyaman na karamar hukuma, kar mu je da nisa, ko mai karatu ya san hatta ‘ya’yan Kansila babu a cikinsu?! Ai kuma manyan Sakatarorin Gwamnati, a matakin Tarayya da Jiha, babu yaranku a cikinsu! Haka, Ambasadodinmu, da ma sauran masu rike da manyan mukaman siyasa ko na aiki, duka babu Yaransu cikin wadancan dake watangaririyar bisa kwalta da sunan masu hayar babura. Babu ma ‘ya’yan Sarakan-yanka ko na Hakimai cikin wadancan Yara. Idan kuwa haka ne, ya dace mai karatu ya yi tsai, yai karatun-ta-natsu cikin wannan lamari!. Domin kuwa, da fantsamar wadancan YARA cikin hayar BABURAN wani abin alheri ne tattare da su a gaba, babu kokwanto, da ‘YA’YAN wadancan MANYA da muka lasafta ne za su mamaye harkar kacokan. Da yake ilmi shi ne gaba da komai, ai kowa ya san irin yadda MANYAN ke riginginton kai yaran nasu makarantu.

Ashe ba abin mamaki ne ba a yau, ka ga Yara ‘yan kasa da Shekaru 18 rike da manyan bindigu, da sunan ‘yan boko haram; ko masu garkuwa da mutane; ko masu yankan aljihu; ko ‘yan jagaliyar siyasa; ko ‘yan daba da makamantansu. Ai kai yanzu mai karatu, da za ka zurfafa tunani, za ka tunano cewa, lokacin da kake munzalin Shekarun wadancan Yara, daga Makarantar boko sai ta Addini ce kake ta kai-kawon zuwa. A can ne ka sami karatu, har kake kallon irin wadancan miyagun halayen da aka lasafta wadannan Yara na yi, da abin-kyama abinda bai dace ba! To me ya sa wadannan yara ma za a rika ganin-bekensu, alhali da gwamnati da sauran masu-ruwa-da-tsaki a yau cikin al’uma, ba a damu da samarwa irin wadannan ‘ya’yan Malam Shehu mafita ba?!.

Gaskiyar magana, dole ne al’uma da gwamnati, su tasamma kange irin wadancan Yara ga barin tsunduma cikin wannan harka ta hayar baburan barkatai, a ganiyar da ya kyautu a ce suna Makaranta ne!. Maganar cewa iyayen wasunsu na cikin halin talauci, ba zama hujjar da za ta halasta musu yini bisa kwalta, tun safiya zuwa dare, tare da yin watsi da Makarantun Addini da na Zamani.

bii- Wajabta Shigo Da Nagartattun Babura Zuwa Cikin Kasa Ba Tarkace Ba;

Babu shakka, suma ababen hawa nagartattu, kan taka muhimmiyar rawa ga mamallakansu, musamman irin wadannan Kekunan Napep da ake magana a kansu.

Idan baburan masu nagarta ne, masu haya da su za su jima suna morar su. Jimawa a na cin-moriyarsu, na nufin, tattalin arzikin masu hayar, zai jima cikin bunkasa ba tare da an gamu da wani kasgaro ba. Sanin kowa ne cewa, gyara-yau gyara-gobe ga abin hawa, ba abin nema ne ba, musamman abin-hawan da aka zubawa-ido, shi ne ma ake so ya samo abin-kalaci.

Hatta ta wasu fuskoki da dama, za a ga cewa, ababen hawa masu inganci, na kashe kaifin samun hadura ainun bisa titi.

Wani abin takaici dake faruwa da irin wadannan babura kirar Keke Napep da ake shigowa da su cikin wannan Kasa, cikin wasu Shekaru da suka gabata, ta tabbata cewa akwai wadanda kwata-kwata ba su da wani inganci sosai. Ta-kai ta-kawo, hatta wata Kungiya da ake kira da, ‘Keke Owners & Riders Association’ sun shigar da korafi, na a tuhumi wadanda suka shigo da wancan Keke Napep din kirar ATUL.

Cikin Jaridar Banguard ta hudu ga Watan Nuwamba, na Shekarar 2010 (Nobember 4, 2010), waccan Kungiya mai suna a sama, ta shigarwa da Hukumar Kula Da Ingancin Kayayyaki ta Kasa, ‘Standard Organization of Nigeria, (SON)’ korafin dake nuna cewa, an shigo da Baburan Keke Napep kirar ATUL, har kimanin guda dubu uku da dari daya da casa’in (3,190) duka marasa inganci, wadanda kudinsu ya tasamma naira miliyan dubu guda da miliyan dari hudu da talatin da biyar da dubu dari biyar (N 1, 435, 500, 000).

Bai dace Najeriya ta zamto tamkar wata Bolar jibge rubabbun kaya ba. Saboda haka, dole ne masu ruwa da tsaki su rika sanya idanu tare da maganin duk wani abu da zai zamewa jama’ar Kasa dan-zani ba. A daidai nan ne ya dace mu ci-burki da irin namu A Daidaita Sahun na Alkalami. Allah Shi datar da mu. Amin.

Exit mobile version