Ibrahim Garba Nayaya" />

Hanyoyin Magance Shaye-Shaye Cikin Al’umma

A duk lokacin da ma’abocin rubuce-rubuce ya dauki alkalaminsa domin yin wani rubutu kan abin da ya shafi matasa, idan ya tsaya tsam ya kare wa rayuwar matasan wannan al’ummar kallo domin tsinkayen kan abin da ya kamata ya yi rubutun, sai ya rasa akan me zai yi wannan rubutun. Ba wai domin matasan ba su da wasu matsaloli ba ne, ko kadan, matasan na tattare da matsaloli, bal ma tarin matsalolin ne ma suka sanya sai a rasa fagen da za a tattauna wannan batu. To amma idan mutum ya nutsu, ya tattara hankalinsa wuri guda, zai yi tsinkaye ga sababin samuwar wannan matsala ga matasa, zai ga shaye-shayen miyagun kwayoyi sun taimaka, ko ma a kira su jigo ga gurbacewar rayuwar matasan. Wannan ta sanya alkalaminmu ba zai gushe ba face yana tattauna wannan matsala domin ci gaba da riskar da dukkanin wanda nauyi ya rataya a wuyansa na al’umma gaba daya.

Idan ana magana a kan shaye-shaye, za mu ga masana da dama sun tattauna wajen bayyana ita kan ta kwayar da kuma abin da ake nufi da shaye-shaye. Misali: Bukarti a cikin littafinsa ya bayyana shaye-shaye da cewa “Shaye-shaye na nufin yin amfani da magunguna ta hanyar da ba ta dace ba, wanda hakan zai iya haifar da illa. Likitoci masu kula da kwakwalwa sun bayyana cewa za a iya kiran mutum dan shaye-shaye matukar ya ki daina amfani da amfani da wani magani duk da sanin irin matsalolin kwakwalwa ko na jiki da wannan magani ke jawo masa”. Ya ci gaba da cewa, “Don haka abin da ake nufi da shaye-shaye shi ne yin amfani da magani don wani dalili sabanin wadda aka samar da maganin dominsa; ko kuma amfani da maganin da yake haramtacce ko kuma wanda ya saba da al’ada da tsarin zamantakewa”. A takaici, sai ya jero wadansu abubuwa da za a iya kallonsu duk a matsayin shaye-shaye.

-Yin amfani da magani ba don inganta lafiya ba.

-Yin amfani da mag ani don infanta lafiya, amma a aha fiye da yadda likitoci sika yi umarni.

-Shan maganin da hukuma ta haramta.

-Shan magani kowane iri ne ba tare da umarnin likita ba.

-Shan maganin da al’ada ta yarda da shi, amma fiye da kima.

Irin wannan bayanin, shi ne makamancin bayanin Gidan Dabino a nasa littafin (Mata da Shaye-shayen Maye: Ina Mafita?) bayan ya bayyana asalin kalmar da shaye-shaye ke nufi a kasar Hausa.

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, wato NDLEA ta bayyana ma’anar kwaya da cewa, “Kwaya ita ce dukkanin wani abu da za a sha ko a hadiya ko a shaka kuma dalilin haka ya kawo canjin yanayin jiki ta hanyar samun kuzari ko kuma ya kawo kasala ko ya haifar da canjin kwakwalwa ko tunani.

A bayanin Gidan Dabino cikin wancan littafin da na ambata, sai ya bayyana ma’anar shan kwaya da cewa, shi ne shan kwayoyi wadanda a likitance bai zama dole ba ko kuma a sha fiye da kima da kuma shan kwayoyi wadanda doka ta haramta a yi amfani da su, kamar: wiwi da hodar Iblis wato cocaine da makamantansu”.

Iran duk mun fahimci wadannan bayanai da na yi a matsayin matashiya ko shimfida, to sai mu koma ga sabuban shaye-shayen da kuma bayyana hanyoyin magance wadannan shaye-shaye tsakanin al’umma.

Za ku yarda da ni idan na bayyana zaman banza da abokan banza su ne jagora ko kan gaba wajen tsundumar matasa maza da mata cikin harkokin shaye-shaye, domin mafi yawa idan wani na sha zai yi iyakacin kokarinsa wajen jan abokanensa sa sha, musamman idan ya ga wani abokinsa na cikin wata matsananciyar damuwa, sai ya yi ta rudarsa da cewar wannan shaye-shayen zai taimaka wajen yaye masa damuwar da yake ciki, ya kuma kawo masa hutu a zuci. To daga nan sai wannan ya fada, shi ma haka zai rudar da wani, wannan sai ya bayu zuwa ga shaye-shayen ya fadadu a cikin al’umma. Daga lokacin da wadannan shaye-shaye suka mamaye al’umma, to sai matsaloli su addabi jama’a, domin shan kwayoyin nan zai gusar da hankalin mai sha ne, karshe ya gigice, kwakwalwarsa ta tabu, sai ya rinka aikata abubuwan da idan da a hankalinsa yake to ba yadda za a yi ya yi su, amma sakamakon gushewar wannan hankali sai ya fada aikata munanan abubuwa.

Sanin kowa ne, shaye-shaye ne sababin yawaitar sace-sace, fyade, ta’addanci, hatta rikicin boko haram, shaye-shaye ya ba da gudumawa, kamar yadda mace-macen aure da kashe-kashe da luwadi ga wasu, shaye-shayen kwaya sun taimaka. Idan aka yi duba ga yan bangar siyasa, za a iske sai sun sha kwayoyi hankalinsu ya gushe, sannan su afka wa wanda aka umarce su. Haka zalika, dukkanin wasu nau’i na yan ta’adda kafin su yi ta’addanci za a iske sai sun yi tatil da kayan shaye-shaye. Uwa-uba, babbar matsala ta karshe da shaye-shaye me haifarwa mai yi, ita ce hauka.

Mu na da sani akwai hukuma mai zaman kanta domin magance wadannan shaye-shaye, wato NDLEA. Wannan Hukuma a wasu lokuta kuma a wasu yankunan sun yi sakaci da aikinsu, bal ma da wasun su ake wannan sana’a. Amma a wasu yankunan, Hukumar na yin aikinta bisa tsari ta yadda za ta kawo karshen wannan al’amari, wanda ba zafafawa da yawa dauri ko horo mai tsanani ne zai magance ta, a wasu lokutan shiga jikin matasan, wayar musu da kai, fahimtar da su muhimmancinsu da muhimmancin rayuwarsu za su taimaka wajen kawo karshen wannan shaye-shaye, ko kuma a samu sauki matuka.

A cikin wannan satin na so buga misalai da daya daga cikin kwamandojin wannan Hukuma ta yadda yake bi domin magance wannan shaye-shaye, domin ya bi tushen abin, kuma an samu sauki sosai na raguwar mashayan. Aminu Idris, shi ne Kwamandan wannan Hukuma ta NDLEA reshen Karamar Hukumar Nguru ta Jihar Yobe, wanda babban abin da ya fara yi tun turo shi wannan gari domin yin aiki, sai ya fara shig cikin matasa, da kai ziyarce-ziyarce wurin sarakuna iyayen kasa, da neman hadin kan kungiyoyi da malaman makarantu, hakan sai ya ba shi damar dakile da yawa daga cikin wannan shaye-shaye.

Wannan bawon Allah, ya yi kokarin shirya taruka da kai ziyarce-ziyarce makarantu domin sanar da yara (dalibai) illolin shaye-shayen. Ban manta ba, na ga yadda ya rinka kai ziyara tsakanin makarantun kudi da na gwamnati, kuma ya nemi a ba shi lokaci, a tara masa dalibai, ya fadakar da su. A duk lokacin da ya kama masu shaye-shaye, yakan bi wani tsari na bibiyar sababin shigar mutum wannan harka, wannan ya sanar masa da illar hakan a rayuwarsa, da kuma amfaninsa a nan gaba. Wannan ya sanya da yawa cikin wadannan mashaya suka daina wannan shaye-shaye, har ma suka kama sana’o’i. Ta fuskar shigowa gari da muggan kwayoyin, hakika ya dakile wannan sana’a matuka gaya, domin ya nemi hadin kan dukkanin wasu jami’an tsaro dake wannan yanki domin su yi aiki kafada-da-kafada a matsayinsu na masu bayar da tsaro da kariya ga al’umma.

Zan Ci Gaba A Sati Mai Zuwa Insha Allah

Nayaya shi ne shugaban kngiyar Nguru Writers’ Association of Nigeria

Exit mobile version