Hanyoyin Magance Warin Baki

Daga Bilkisu Tijjani Alkassim,

Uwargida ko kin san yadda za ki magance warin baki da kuma yadda za ki maida hakoranki su zama farare? Uwargida ki kasance mai kokarin gyaran bakinki a kowane lokaci kar ki zama wadda ba ta kula da bakinki, ya zama idan kina magana maigida yana kau da kai, ko kin je sumbatarsa amma kuma yana kau da kai, ki zama mai kula da hakoranki a ko da yaushe, za ki iya wanke bakinki da safe da rana da ki dunga wanke bakinki daddare, idan za ki kwanta ko kuma bayan Sallar Isha.

Idan kuma hakan bai samu ba ki dingna wanke bakinki da safe da kuma dare, kar ki yarda ki je waean maigida ba wankin baki, saboda duk abin da kika ci yana makalewa ne a cikin hakoranki da zarar baki wanke baki ba kika kwanta.

to za ki ji bakinki yana wani wari sai ki ga maigida yana kau da kai idan kuna tare, sannan bayan kin wanke hakoranki da daddare uwargida ki samu kanun fari kamar daya ko biyu sai kisa a bakinki kina dan tauna shi kadan-kadan haka yana sa kamshin baki kafin ki kwanta za ki ji bakinki yana kamshin kanunfari.

Uwargida idan kika koma amfani da kayan gida wanda yake sa hakori fari iyayan mu na da suna amfani da gawayi wasu kuma da yashi ko kuma toka, iyayammu suna wanke bakinsu da gawayi kuma sun ce ma ya fi makilin fitar da hakori.

Yadda suke wanke bakinsu da gawayi :

Suna daka gawayin sai su sa masa jar kanwa kadan a ciki su hada su su yi ta dakawa har sai ya yi laushi sosai ya koma gari sai su ajiye shi su rika diba kadan-kadan suna wanke bakinsu da safe da kuma yamma. Wasu kuma sai su hada biyu da makilin bayan sun wake da gawayi, saboda ya yi kamshi, idan uwargida za ki rika wanke bakinki da wadannan abubuwan ke da warin baki kunyi bankwana sannan kuma hakoranki za su yi fari sosai .

Ita kuma toka yadda ake amfani da ita , ita ma za ki gyarata ki tsintsince komai na cikinta, wasu har tankade ta suke yi, bayan su gyara ta sai su ajiye ta su diba da kadan-kadan suna wanke bakinsu suna sa danyatsrsu suna dangwala suna dirje ahakoransu, shi ma yana sa su yi fari sosai.

Sannan kuma wasu suna amfani da bekin soda, idan uwargida kika samu bekin soda za ta taimaka wajan haskaka hakoranki a cikin wani dan kankanin lokaci.

Yadda za ki yi amfani da bekin soda shi ne:

za ki jika burushinki da ruwa wanda kike goge bakinki da shi, sannan ki dangwala shi cikin baikin sodar sai ki dangwalo sannan ki goge bakinki da ita kamar yadda za ki wanke da makilin, idan kika gama za ki ga yadda hakorinki zai yi fari sosai, amma ba kullum za ki wanke da baikin sodar ba, saboda za ta iya lalata dadashin hakori. Saboda haka uwargida kar kii mayar da ita abin wanke baki kullum za ki iya amfani da ita kamar sau biyu a sati.

Sannan kuma uwargida ki guji cin abin da zai dafar miki da hakoara wanda zai sa hakorinki ya yi baki

Exit mobile version