Rabiu Ali Indabawa" />

Hanyoyin Neja: ’Yan Majalisa Sun Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Bada Biliyan N50

An bukaci gwamnatin tarayya da ta sama da kudade na musamman kimanin naira biliyan 50 domin gyaran hanyoyi a Jihar Neja.

‘Yan majalisa a majalisa wakilai ne suka bukaci a bayar da kudade na musamman domin aiwatar da hakan.

A cewar ‘yan majalisar, a kamata a samar da kudaden ga hukumar da ya kamata ta shirin cigaba na shugaban kasa. ‘Yan majalisar sun wannan kira ne ga gyaran hanyoyi a jihar Neja a zaman majalisa na ranar Alhamis, 7 ga watan Nuwamba. Kazalika ‘yan majalisar sun bukaci gwamnatin tarayya da ta samar da kudade na musamman na naira biliyan 50 domin gyara hanyoyin.

A cewar ‘yan majalisar, ya kamata a samar da kudaden ga hukumar da ya kamata ta shirin cigaba na Shugaban kasa. A wani korafi da dan majalisa na jam’iyyar (APC), Sa’idu Abdullahi (Jihar Neja) ya shigar, ya ce an bayar da kwangilar wasu hanyoyi kamar su Bida-Lambata, Minna-Suleja, Tokwa-Tegina-Makera-Kaduna. Abdullahi, a aorafin wanda sauran ‘yan majalisa takwas daga jihar Niger suka hada hannu, ya ce an bayar da kwangilar ne ga kamfanonin gine-gine daban-daban don cimma manufa.

Ya ce lokacin da aka diba domin kammala aikin gyare-gyare ya kasance sama da watanni 18 zuwa 36 kuma tuni ya dade da cika.

A cewarsa, aikin da aka yi zuwa yanzu bai wuce kaso 20 cikin 100 ba tun da aka bayar da kwangilan. A baya rahoto sun tabbatar da cewa Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, SAN, a ranar Laraba ya jaddada cewa, titunan Nijeriya ba su yi lalacewar da kullum ake magana a kai ba. Yayin da ya yi magana da manema labarai jim kadan bayan fitowarsa daga taron majalisar zartarwa ta tarayya da aka yi ranar Laraba, ya ce ana zuzuta rashin kyan titunan Najeriya ne kawai. Taron majalisar zartarwar da ya samu shugabancin mataimakin shugaban kasa, farfesa Yemi Osinbajo, ya aminta da yin titunan Bida zuwa Sachi zuwa Nupeko da gadar Nupe ko zuwa Patigi da ke kan kogin Niger, wacce ta hada Nupeko da Patigi a jihohin Niger da Kwara.

Exit mobile version