Hanyoyin Ruwan Nijeriya Sun Zama Masu Hadari – Hon. Hamisu

Hon. Hamisu Ibrahim

Daga Bashir Bello

Majalalisar wakilan Nijeriya ta bukaci ma’aikatar sufuri da sauran hukumomin da ke karkashinta da su tabbatar da ka’idojin kiyaye haddura a duka hanyoyin ruwa dake Nijeriya.

Bukatar hakan na kunshe ne a cikin wani kudirin doka da ya bukaci samar da kiyaye haddura a  hanyoyin ruwa na Nijeriya, wanda Hon. Hamisu Ibrahim mai wakiltar mazabar Kubau/Ikara a Jihar Kaduna ya gabatar a zaman majalisar na ranar Talatar nan.

Da yake gabatar da kudirin Hon Hamisu Ibrahim ya ce ruwa hanya ne na sufuri a Nijeriya, amma a yan kwanakinnan hanyoyin ruwan Nijeriya sun zama masu hadari, inda rahotanni suka yi nuni da cewa sama da mutane 300 ne suka rasa rayukansu yayin da aka sami hasarar rayuka sama da 100 daga watan Mayu zuwa Satumbar, 2021.

Ya ce hadduran jiragen ruwa a Nijeriya na faruwa ne sakamakon daukar kaya ko mutane fiye da kima, da rashin Kula da lafiyar jiragen ruwa da kuma gudun wuce sa’a kana da tukin ganganci da  mummunan yanayi.

Ya kara da cewa idan za a iya tunawa a ranar 26  ga watan Mayun 2021 wani jirgin ruwa dauke da mutane 160 ya rabe biyu kana ya nutse a Kogin Neja, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 100 sannan a 27 ga watan Satumbar, 2021 wani hadarin jirgin ruwa ya faru a jihar Lagos dake Kudu maso yammacin Nijeriya, inda aka tabbatar da mutuwar mutum daya bayan da jirgin ruwan ya kife.

Har ila yau majalisar ta bayyana damuwarta dangane da karuwar hadarin jiragen ruwa a hanyoyin ruwa na kasar sakamakon karya dokoki da kaidodi da masu sufurin ke yi, inda suke daukar fasinjoji fiye da kima a kokarin da su yi na samun kudin shiga.

Hon. Hamisu ya kara da cewa za a iya kiyaye hadduran jiragen ruwa ta hanyar wayar da kan jama’a sananna hukumomin dake Kula da hanyoyin ruwa su tabbatar da bin ka’idodi a hanyoyin ruwa, da kula Lafiya jiragen ruwa a kai a kai kana da yashe dattin dake cikin ruwa.

Daga karshen majalisar ta bukaci Ma’aikatar Sufuri da hukumomin dake karkashinta da su tabbatar da bin kaidodin kiyaye haddura a duka hanyoyin ruwa na Nijeriya.

 

Exit mobile version