A wannan makon za mu kawo muku hanyoyin ake bukata mai sha’awar shiga harkar noma ya xauka domin samun cikkakiyar nasarar da ake bukaka, wadda hakan zai taimaka wajen ci gaba da bunkasar nomad a tattalin arzikin kasa.
Wannan shafi mai albarka na Noma tushen arziki inda mukan tattauna al’amuran da suka shafi noma da kiwo tare da yin tsokaci kan waxansu muhimman bayanai na masana da nufin yin bayani dalla-dalla a kansu, domin faxakar da manoma na birni da karkara kan yadda za su samun karfin gwiwar ci gaba da gudanar da muhimmiyyar sana’a ta noma da kiwo da muka gada tun iyaye da kakanni. Allah kaxai muke roko ya karba mana kuma ya inganta mana kasar nomanmu da kiwo domin ci gaban tattalin arzikin wannan kasa tamu mai tarin albarka. A yau da yardar za mu tattauna ne a kan waxansu hanyoyi ko dabaru muhimmai a kan yadda masu wannan harka ta noma da kiwo za su kai ga bunkasa sana’arsu.
Yana da kyau ga duk mai niyyar shiga wannan harka ta noma da kiwo ya kwan da sanin cewa akwai haxurra da ke cikin wannan harka wanda hakan ke nuna cewa samun nasara a cikin ya ta’allaka kacokan ga sa’a da kuma bin abubuwa sau da kafa. Samun nasara a wannan harka ta noma da kiwo ya dogara da irin hangen nesa da kuma kyakkyawan tsari wajen gudanar da wannan harka mai tsananin riba. Fara wannan harka ta noma da kiwo zai ba wa mutum damar da yake bukata ta zama mai dogaro da kansa, amma kafin ka kai ga fara wa ya kamata ka fara bincikar kanka ta hanyar da za ka gane inda kake da karfi da kuma inda kake da rauni wajen gudanar da wannan harka ta noma da kiwo. Saboda haka yana da kyau ka tambayi kanka waxannan muhimman tambayoyi wanda ba da amsarsu zai taimaka maka sosai wajen shiga wannan harka ko dakatar da shiga zuwa wani lokaci nan gaba.
Shin Wannan Shi Ne Karon Farko Da Za Ka Fara Noma?
Kasancewar ka sabo a wannan harka yana da kyau ka zama ka samu dukkan karfi da zuciya da za ka iya jurewa wannan aiki, da kuma xaukar muhimman tsare-tsare da za su taimaka wa ci gaban wannan harka ta noma da kiwo. Harkar noma da kiwo na bukatar kwazo da aiki tukuru, yana bukatar kokari da juriya da zai ba ka damar yin aiki mai yawa a kowacce rana wanda ba za su yi wu ba har sai ka tursasawa kanka yinsu.
Wace Irin Mu’amala Kake Da Ita Da Sauran Mutane?
A matsayinka na manomi nasararka tana da alaka da yadda dangantakarka ta kasance da sauran mutane, waxanda suka haxa da sauran yan’uwa manoma, abokan ciniki da cibiyoyin bincike kan harkar da ta shafi noma da kiwo da dillalai da bankuna da lauyoyi da masana harkar shige da ficen kuxi da mutanen garinku da kuma sauran al’umma. Yana da kyau ka tabbatar ka fitar da nagartattun hanyoyi da za su taimaka wajen biyan bukatun abokan cinikinka.
Shin Ka Iya Xaukar Matakai Masu Kyau?
Ana gane shugaba ne ta hanyar xaukar matakai masu kyau, don haka ana bukatar manoma su dinga xaukar matakai a kan lokaci da cikin gaggawa, domin tabbatar da samun nasara a wannan harka ta noma da kiwo.
Samun Karfi Na Zahiri Da Karfin Zuciya Na Iya Gudanar Da Wannan Harka
Gudanar da harkar noma da kiwo na bukatar mai da hankali kacokan ga mai gudanar da wannan harka. Babu batun buya ko labewa ga mai yin wannan harka a matsayin ta na yar lelenka. Ko uwa tana guduwa wajen shayar da ‘yarta ne? Kasancewarka a wannan harka yana da daxi duk da cewa akwai ayyuka masu yawa da kalubale. Dole ka tsara lokutan ayyukanka, amma a lura duk abin da ya kamata a yi a tabbatar an yi shi a kan lokaci cikin gaggawa.
Samar Da Kyakkyawan Tsarin Gudanarwa
Kamar yadda muka sani cewar rashin tsari shi ne babban abin da yake rugurguza yawancin harkoki ba ma kawai na noma da kiwo ba. Ka sani cewa tsarin gudanar da harka mai kyau yana taimaka wa wajen kauce wa haxurra masu yawa.
Yanayin Dagewarka Kan yadda Kake Gudanar Da Al’amura
Gudanar da harkar noma na da wahalar gaske, wanda wannan zai iya janyo wa mutum gazawa a waxansu lokutan. Saboda yawancin mamallakan wannan harka sukan gaza wajen xaukar nasara ko rashinta. Don haka kana bukatar ka dinga samun karfafa gwiwa a kowanne lokaci don ci gaba da xorewar wannan harka, da kuma kariya daga gurguncewar harkar da makamantansu. Domin kuwa da wannan harka tana da sauki gaya da ka ga kowa a cikinta. A nan ya kamata mu ari karin maganar nan da take cewa idan kana son ka yi sukuwar sallah a wannan harka ta noma da kiwo, dole ka zamto ka shirya faxuwa daga kan dokinka sau shurin masaki ba tare da ka karaya ba.
Yadda Harkar Noma Zai Shafi Iyalanka
Babu tantama cewar a farkon lokacin da ka fara wannan harka za ta xan shafe ka da yadda kake gudanar da harkokin iyalanka ta bangaren kuxi. Wannan kuwa kan iya xaukar watanni kai har shekaru ma kafin a kai ga fara cin riba. Don haka wajibi ka shirya yadda za ka xan gyara yadda kake gudanar da waxannan harkoki domin samun alheri mai yawa nan gaba kaxan.
Ka Xau Wadataccen Lokaci Kana Nazari A Kan Wannan Harka Don Gano Alheri Da Ke Ciki
Ka sani za ka shiga harkar noma da kiwo ne da nufin samun alheri. Don haka kada ka yi gaggawa ba tare daka shirya fuskantar kalubalen dake tattare da wannan harka ba. Yana da kyau ka halarci tarurruka na karawa juna sani da sayen littafai na harkokin noma da kiwo da jaridu da mujallu domin karaka kan ka ilimi a kan harka nomad a kiwo.
Shin Kana Da Gogewa Kan Irin Harkar Da Za Ka Gudanar?
Yawancin waxanda suka ci gaba su ka yi kaurin suna a wannan harka sun kasance suna da gogewa a wannan harka tun kafin su kai ga shiga cikinta ka’in da na’in. Ka halarci lakcoci kan wannan harka tun kan ka kai da fara wannan harka.
Shin Kana Da Karfin Jari?
Rashin kuxi yawanci shi ne kashin bayan karaya ko gurgunta yawancin harkokin kasuwanci ba wai kawai noma da kiwo ba. Don haka kana bukatar jari wadatacce domin gudanar da wannan harka yadda ya kamata.
Shin Kana Iya Sayarwa?
Kowanne iri harkar kasuwanci na bukatar abokan hulxa wato, wanda ake bukatar ka ka fara tuntuba tun farkon lokacin fara gudanar da wannan harka. Yana da kyau ka yi kokari kan bunkasa bangaren da ya shafi saye da kasuwanci na wannan harka domin kuwa in dai hajar ka ba ta karbu ba to kuwa wannan ya zama abin da ake kira an yi ba ai ba.
Da waxannan muhimman bayanai muke ganin duk wanda ya samu damar aiwatar da su yadda ya kamata, zai shiga wannan harka da fatan samun nasara gwaggwaba nan ba da daxe wa ba. Allah ya sanya albarka ya taimake mu a kan dukkanin al’amuranmu na alkhairi kuma ya datar da mu a kan yin daidai, mu samu cin moriyar kokarin da muka yi.