Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Hanyoyin Taimaka Wa Abokin Zama Daina Shan Giya

by
3 years ago
in NAZARI
4 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Labarai Masu Nasaba

Ahuwar Rashawa Ga Dariye Da Nyame Na Ci Gaba Da Yamutsa Hazo A Nijeriya

Zaben 2023: Yadda Bangaranci Da Bambancin Addini Ke Kokarin Tayar Da Kura

Kasancewa tare da abokin zama mai shan giya kan iya zamo wa mugun abu ga dayan abokin zaman, ya zamo abun da zai iya taba rayuwarsa da takura a gare sa, shin ya kasance abokin zaman sa ne/ta da aure, ko kuma da ko diya ne ke shan giyar, ko ma dai wanne ne daga ciki.
Shan giya kan haifar da matsaloli ga mai shan giyar daban-daban, matsalar lafiyar jiki ce, ko kuma ta kwakwalwa, wani lokaci, matsalar ta kan shafi abokin zaman sa.
Ba wannan kadai ba, shan giya na da illa ga tattalin arzikin mutum. Mai shan giya kan iya rasa aikin sa, ko kuma wani abu da yake gudanarwa na harkokin rayuwarsa.
Saboda haka, wasu lokutan, ya kan zama dole ga abokin zama ya jure hakurin zama da mai dabi’ar shan giyar ko da ba dadi.
To sai dai kuma, ba iyakar ta nan ba, akwai hanyoyi da mutum zai iya bi wurin taimaka wa abokin zaman sa wurin ganin cewa ya daina wannan dabi’ar shan giyar.
Akwai matakai daban-daban da mutum ka iya dauka don taimaka wa abokin zaman sa, ga matakan kamar haka:
Sanin Illar Giyar
Dai daga cikin matakan farko da abokin zama zai bi shi ne ya fara gane shin minene illar giyar ma, mi take haddasawa, wane irin cutatawa mai shan ta take yi?
Ita dai giya, cuta ce da in ta kama mai shanta, to ba karamin abu ke sa ya daina ba. Giya ta kan zame wa mai shan ta jiki sakamakon yawan shan da yake a kan duk wani abu da zai yi, da jin cewa shi ba ma zai iya yin wani abu ba tare da ya sha ba, ba wai lalle sai in yana sha da yawa ba ne ta kan iya kama mai jiki ba; a’a yawan sha dai.
Shan giya kan haifar da wasu abubuwan ki a cikin gidan mashayin, ga matarsa ne, ko yayansa, misali, akwai rashin iya yin aiki yanda ya kamata, tare da mugun kiuya, matsalar zamantakewa a cikin gida da iyalinsa, da kuma rashin maida hankali ga abubuwan da ya kamata a matsayin sa na uba sakamakon gushewar hankali, mashayin giya, akasari ya kan zama baya girmana komai baya ga giyar.
Ga wahalhalun rayuwa, ga matsalar shan giya, wani lokaci hakan kan haifar mashayi ya iya samun matsalar tunani ko kwakwalwa, wanda hakan kan iya haifar masa da matsala da abokan aikin sa, yan uwan, abokai ko ma iyalinsa
Tattaunawa Dashi
Daga cikin wasu hanyoyin da ya kamata mace ta bi ga mijinta, akwai tattaunawa da shi kan abin da take hange kan halin na sa, da kuma damuwarta kan lamarin. Na’am, ba mamaki kin sha masa magana a kai, to amman ba laifi da ci gaba da nanata ma sa, kamar yanda masanin hallayar dan adam, Farfesa Oni Fahboungbe ya fada cewa, a cikin matakan farko na kokarin shawo kan mashayin giya, akwai bukatar tattaunawa da lurar da shi.
“A dukkan matakan ganin an jawo hankalin mashayi ya daina, to tattaunawa na kan gaba,” inji Farfesan.
An san cewa dole ne akwai bacin rai da damuwa ga wanda abokin zaman sa ya kasance mashayi, to amman duk da haka, abin da ya fi kamata, maimakon nuna masa tsana da tsangwama, to a janyo shi a jiki tare da fadakar da shi illar yin hakan. Zagi da fada, ba shi ne abin da ya fi dacewa ba, inji Farfesan.
Farfesan ya ci gaba da bayani da cewa, tsangwama da fada ba zai kawo komai ba face turjiya daga shi mai aikata abun, wato mashayin.
“A cikin kokarin ka/ki na janyo hankalin sa, dole ne a kauracewa yin anfani da matakin fada, kushe ko tofin alla-tsine,” inji Farfesa masanin hallayar dan adam.
Wani lokaci, a kokarin ki na janyo hankalin sa, akwai bukatar ki nuna masa kamar ma ai ba laifin sa ba ne yin shaye-shayen, kilan kaddarace, jarabawa ko wani abu makaimaicin wannan.
Matsalar tsangwana, ko tofin alla-tsine shi ne, za ki sa shi ya ji kamar kin tsane sa, saboda haka, zai fara ganin kamar ma ke makiyarsa ce, Saboda haka, bai kyautu tsangwama da kushe ba, inji shi.
Farfesan ya ci gaba da cewa, a kokarin shawo kan shi, za ki iya kirkiro labari na wani mai irin wannan dabi’ar, da yanda karshen sa ya zama, ba dan komai ba sai dan ankarar da shi.
Neman Taimakon Likitoci
Har wa yau, za a iya kai sa asibitin shawararwari da ladabtarwa ta kwararru kan dan halayyar dan adam, to amman, dole a dauki matakai na siyasa, domin sau da yawa, masu Shaye-shaye basa yarda da suna da matsala.
Cikin hikima da dubara kuma, idan sun ki, za a iya nuna masu za a dauki mataki, kilan ki ce ke za ki tafiyarki, ko da hakan zai kaikaito shi kenan.
Musanya Shan Giyar Da Wani Abu
Baya ga daukar matakin likita da kwararru, to a kashin kan ki, za ki iya daukar wani matakin na samar ma sa da dan wani abu na sha, a maimakon giyar, mussamman ma idan ya zama shi kansa yana da ra’ayin barin. To amman fa, abun ba zai zama kamar giya ba da ke bugarwa.
Farfesan ya kara bayani da cewa, duk lokacin da mutum ya zaku sosai da shan giya, to fa hakan na nufin za ta zame ma sa jiki, ta yadda ba ya iyawa sai da Ita. Yanzu idan ma bai sha ba, zai zama baya jin dadin rayuwarsa. Duk da cewa akwai illa, amma zai zamar ma sa dole yin hakan.
Farfesan ya ce, “Idan har za a raba su da wannan dabi’ar, to dole ne a fara canza masu Ita wannan dabi’ar da wata daban, akwai kuma hanyoyi daban-daban na yin wannan.
A nan ne Farfesan ya ce, “Abu mai muhimmaci shi ne fara raba su da waccan dabi’ar, sannan daga baya, sai a samar masu da wani abun sha ba mai bugarwa ba, kamar dan wani abun sha haka ba mai dauje da kwaya ba amman.”
“Da zaran an samu nasarar raba shi da shan giyar, sai a yi gagagwar musanya masa da wani abun daban,” inji shi.
“Bayan yin wannan, a daidai lokacin da ya dan daina shan giyar, to sai a fara ankarar da shi hadarin hakan, da sannu zai fara kaucewa waccan dabi’ar da kan sa,” inji shi.
Matakin Kula Da Kai
Idan har ya zama shan da yake yana da barazana ga rayuwarki da ta yayan ki, to ki nemi mafaka da mabuya da ke da sauran yaran duk lokacin da wani abu zai faru. Duk wasu matakai da ya kamata, to sai ku dauka domin tsira.

ADVERTISEMENT

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Mahimancin Taimako

Next Post

Barace-baracen Kananan Yara A Birane Abin Dubawa Ne

Labarai Masu Nasaba

Dariye Da Nyame

Ahuwar Rashawa Ga Dariye Da Nyame Na Ci Gaba Da Yamutsa Hazo A Nijeriya

by Idris Aliyu Daudawa
1 month ago
0

...

Bangaranci

Zaben 2023: Yadda Bangaranci Da Bambancin Addini Ke Kokarin Tayar Da Kura

by Muhammad Maitela
2 months ago
0

...

Tsakanin Tiktok Da Facebook: Nazari Kan Tasirin Bidiyo A Kafafen Sadarwa

Tsakanin Tiktok Da Facebook: Nazari Kan Tasirin Bidiyo A Kafafen Sadarwa

by
3 months ago
0

...

Wace Illa GB WhatsApp Ke Da Shi?

Wace Illa GB WhatsApp Ke Da Shi?

by
7 months ago
0

...

Next Post
Barace-baracen Kananan Yara A Birane Abin Dubawa Ne

Barace-baracen Kananan Yara A Birane Abin Dubawa Ne

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: