Har Sarkin Bai Ya Koma Ga Allah Shi Al’ummar Danbatta Ke Kallo A Matsayin Hakimi – Karibu Abdulkadir Dantata

Daga Ibrahim Muhammad Kano,

An yi kira ga Gwamnati a kan ta daina siyasantar da harkar Sarauta domin abu ne na gado, na gargajiya da ake tafi dashi tun kafi Turawa su yi tunanin zuwa kasarnan da kuma al’umma suke martabasu.

Alhaji karibu Abdulkadir Dantata a bayyana hakan a Kano da yake zantawa da yan jarida.

Ya ce abin takaici ne ganin yadda Gwamnati saboda son kai na siyasa kawai, ta zo ta sukurkuta harkar Sarauta ta kawo sauye sauye da basa yi wa al’umma dadi.Saboda ana dauki dora kamar yadda aka yi a Danbatta ,wanda duk da haka a Danbatta har Sarkin Bai Alhaji Muktar Adnan ya koma ga Allah mutane shi suke kallo a matsayin Hakimin su ba wani dauki dora ba.

Ya ce siyasa ta sa ana ragewa sarauta daraja ya zama basa fada aji, amma da abin yadda yake ne a baya babu siyasa in wani abu ya taso masarauta ake sawa ta yi magana da al’umma za su karba nan da nan, amma yanzu ace wannan yana tare da wannan baya tare da wannan.
Ya ce har gobe mutane suna ganin kimar sarauta da mutuntaka.

Alhaji karibu Abdulkadir wanda daya ne daga cikin jikokin Marigayin ya ce rasuwar Sarkin Bai abu ne da ya daga zuciya duk kuwa da cewa kowa na hakan makomar kowane, sai da mu yi fatan Allah ya jikansa ya gafarta masa. Tabbas mutum ne mai kyakkyawan mu’amala da mutane da girmamawa, su jama’ar danbatta shaida ne a kan haka.

Exit mobile version