Duk da cewa an dakatar da dukkan wasannin kwallon kafa a nahiyar Turai da wasu sassan
duniya saboda annobar cutar coronabirus wadda ta addabi duniya a wannan lokacin amma ana
ci gaba da wasanni a kasar Belarus.
A baya can ba kasafai ake maganar gasar kwallon kafar Belarus ba, amma yanzu tana bakin
mutane ganin ita ce tilo a Turai da ke ci gaba da gudanar da harkokin kwallon kafa duk da cewa
duk wani wasa ya tsaya.
A ranar Asabar an buga manyan wasanni shida a kasar har da wasan hamayya tsakanin FC
Minsk da Dinamo Minsk, wanda mutum dubu uku (3,000) suka kalli karawar a babban birnin
kasar.
Kasa da mutum 100 ne suka kamu da coronabirus a kasar, wadda babu wanda ya mutu a kasar
mai mutum miliyan 9.5 sai dai har yanzu kungiyoyi da dama a duniya suna kira ga hukumar
kwallon kafa ta duniya data dakatar da wasanni a kasar.
Ya yin da kusan baki dayan Turai suka killace kansu da rufe iyakokinsu, shi kuwa shugaban
Belerus, Aledander Lukashenko bai damu ba, inda ya yi kira da yan kasa su sha barasa “Vodka”
don yakar coronabirus.
Sai dai shugaban hukumar kwallon kafar Belerus, Aleksandr Aleinik ya ce sun dauki matakan da
suka dace kan dakile yaduwar coronabirus shi ya sa suka ci gaba da wasannin kwallon kafa
kuma idan aka samu wani dan wasa daya kamu zasu dauki matakin daya dace.