Connect with us

WASANNI

Har Yanzu Akwai Aiki A Gabanmu, Cewar Ahmad Musa

Published

on

Kwallo biyun da dan wasa Ahmed Musa ya zura a minti na 49 da 75 sun bai wa Super Eagles ta  Najeriya damar doke kasar Iceland da ci 2-0 a gasar kofin duniya a wasa na biyu da kasashen biyu suka fafata.

Wannan nasara ta bai wa Super Eagles damar hada maki uku bayan wasa biyu bayan kuma tayi rashin nasara a wasan farko da kasar Crotia a satin daya gabata.

Kuma a yanzu Najeriya ita ce ta biyu a rukunin bayan Croatia wacce tuni ta kai mataki na gaba bayan da ta doke Argentina da ci 3-0 a ranar Alhamis.

A yanzu Ahmed Musa shi ne dan kwallon da ya fi kowanne ci wa Najeriya kwallo a tarihin gasar cin kofin duniya, inda ya zura kwallaye hudu.

Najeriya za ta kara da Argentina a wasan ta karshe na rukunin D domin fayyace kasar da za ta bi Croatia domin zuwa zagayen kifa-daya-kwala wato zagaye na biyu na ‘yan 16.
Advertisement

labarai