Har Yanzu Akwai Kutare Miliyan Biyu A Duniya – Dr. Tsanyawa

Daga Mustapha Ibrahim Kano,

Yanzu haka Aduniya akwai masu dauke da cutar kuturta da suka haura miliyon biyu, wadanda suka kai adadin 2,021,890 a duniya, sai kuma yanki kasashen Afrika ke da adadin kutare kimanin 20,209, sai Najeriya mai yawan kutare 2,424, haka kuma Jahar Kano na dauke da adadin masu cutar kuturta kimanin 118.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Kwamishinan Lafiya na Jahar Kano, Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa, a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano a ranar Litinin da ta gabata. wacce ita ce ranar yaki da cutar kuturta ta duniya, kamar yadda hukumar kula da lafiya na Majarisar Dinkin Duniya ta ware, don yaki da kuma tausayawa masu dauke da wannan larura a fadin duniya.

Dr. Tsanyawa wanda ya yi dogon bayani kan mahimmancin wannan rana da kuma yadda Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya dauki matakin yaki ta wannan cuta da sauran cututtuka a Kano, ya ce, wannan abun a yaba ne ga Gwamnan Kano, musammam irin manyan asibitoci da aka gina irin asibitin Zoo Road da na Giginyu ga kuma cibiyar kula da cutar daji da babu mai girma da kayan aiki irin na cibiyar a Afrika bakidaya da dai sauran abubuwa na bunkasa lafiya masu a kano a cewar Kwamishinan Lafiya na Kano.

Har ila yau ya ce akwai kuma cibiyoyi na jinkan alumma irinsu Gidauniyar Ganduje da ta Dangote da dai sauransu masu talafawa a harkar lafiya sun yi namijin kokari wajen tallafa wa alummar Jahar Kano kamar yadda ya kamata. Haka kuma ganin adadin yawan masu dauke da larurar kutirta a Kano Gwamnatin kano ta tsaya tsayin daka wajen baiwa masu wannan larurar magani kyauta haka kuma wannan ranama ta yaki da cutar sai da Gwamnatin Kano ta rabawa kutare kimanin 100 takarma da man shafawa da dutsan Gwangwarasa na goge kaushi ga kutaran domin dai talafamusu wanda akayi a harabar asibitin yaki da kutirta da sauran cutitka masu alaka da fata da ke asibitin bela da ke Kano.

Shi ma Alahji Isyaku Sarkin Kutaren Kano a jawabonsa da harshen Turanci a asibitin Bela ya bayana gamsuwarsa da yadda Gwamnatin Ganduje ta ke kula da su ta hanyar basu magunguna kamar yadda ta kamata ga kuma yadda yanzu haka aka kawomusu tallafi a wannan lokaci daga Gwamnatin Kano da dai sauran yabawa da sarkin kutaran ya ma Gwamnatin Kano koda yake sarkin kotaran ya bayana yadda suke fuskantar matsala alokacin zafi fiye da lokacin sanyi a yanayin jikinsu sai dai wakilinmu ya rawaito mana cewa masu dauke da wannan larura na daga cikin masu hatsarin saurin kamuwa da Korona fihe da sauran muta ne lafiyayo kamar yadda Dr Tsanyawa ya tabatar da haka.

Exit mobile version