Rabiu Ali Indabawa" />

Har Yanzu Ana Sayar Da (DATA) Kan Tsohon Farashi Duk Da Ragin Kashi 50

DATA

Yawancin masu amfani da layin sadarwa sun ce har yanzu suna sayen ‘Data’ a kan farashin da suka saba, bayan an yi tsammanin farashin ya fadi da kashi 50 cikin 100 ta hanyar umarnin gwamnatin tarayya. Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Dokta Isa Ali Ibrahim Pantami, ya ce an rage farashin Data na 1 gigabait(GB) daga Naira 1,000 zuwa Naira 487, da ka fara daga Nuwamban 2020.

 

Pantami ya ce hakan ya yi daidai da umarnin da ya bai wa Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) kan hakan. ‘Matsakaicin farashin Data 1GB ya ragu daga Janairun 2020 na Naira 1,000 zuwa Naira 487.18 a watan Nuwamba, 2020,’ Ministan ya fada a cikin wata sanarwa ta hannun Mataimakin sa na Fasaha, Mista Femi Adeluyi.

Ya ce rage kudin ya samo asali ne daga aiwatar da shirin nan na yada zango na kasa (2020 zuwa 2025) wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar a ranar 19 ga Maris, 2020. “Daya daga cikin manufofin shirin shi ne a rage matsakaicin kudin Data 1GB zuwa matsakaicin kudi Naira 390 zuwa 2025.

 

“Dangane da Rahoton da NCC ta bayar kuwa, matsakaicin farashin Data zuwa Nuwamba 2020, ya kasance Naira 487.18, wanda ya kai kashi 47.33,kasa da kimar da aka tsara. “Rahoton ya kuma nuna cewa kudin Data a Nuwamba2020 bai kai kashi 50 na kudin Data a watan Janairun 2020 ba.”

Duk da haka, a cikin wani sabunta binciken da majiyarmu ta yi, masu amfani da bayanan sun ce ikirarin cewa kudin data ya ragu kashi 50 cikin 100 ba gaskiya bane, domin har yanzu suna sayen 1G a kan Naira 1000, wata daya bayan sanarwar. Yemi Adeolu a Legas ya ce har yanzu ba’a farashin Data. “Da alama masu aikin ba su yarda da wannan umarnin daga gwamnati ta ba su ba; har yanzu farashin Data har yana nan kamar yadda yake a baya,

 

Musliyu Ladipo, shima ya soki ikirarin. “Kodayake na lura cewa masu aikin yanzu suna ba da wasu karin gigabayita matsayin kyauta, amma farashin har yanzu yana nan.” Akwai kuma irin wannan martani daga Francis Dikwe, wani mazaunin Legas.

Shi ma a nasa tsokacin, da yake tsokaci, shugaban kungiyar masu amfani da layin sadarwar na kasa (NATCOMS), Cif Deolu Ogunbanjo ya ce akwai ragin da aka samu a bangaren fasaha saboda masu gudanarwar sun kara kudin Data ne kawai don tsohon farashin. “Misali wasu daga cikinsu sun kara Naira 1000 daga 1G zuwa 1.5G.”

Ya ce ragin farashin ba batun ba ne amma ya kamata gwamnati ta katse a kan ingancin ayyuka daga kamfanonin sadarwa. A halin da ake ciki,kungiyar Masu lasisin Sadarwar ta Nijeriya (ALTON) ta ce umarnin Gwamnatin Tarayya ya kasance na kama-karya ne kuma zai iya korar masu saka jari.

Shugabanta, Injiniya Gbenga Adebayo ya ce: “Mun sha fada a lokuta da dama cewa idan manufofi suka tsoma baki kan harkokin kasuwanci masana’antar za ta kasance cikin hadari. “Don isa kan tabbatar da an zartar da aiki da farashin, NCC na gudanar da bincike, kuma bayan duk hakan zai daidaita farashin kasar bisa la’akari da abin da aka samu a wasu yankunan.”

Lokacin da aka tuntube shi, NCC ba ta amsa nan da nan ba, amma wani babban jami’i wanda ya yi magana cikin karfin gwiwa ya ce ba Hukumar ce ta yanke shawarar rage kudin Data ba. Jami’in ya ce: “Watakila shi ya sa telcos ba sa yi masa biyayya gaba daya.”

 

Exit mobile version