Abba Ibrahim Wada" />

Har Yanzu Ana Tattaunawa Tsakanin Dortmund Da Manchester United Akan Sancho

Ana ci gaba da neman hanyar da za’a daidaita tsakanin kungiyoyin Manchester United da Borussia Dortmund akan yadda za’ayi cinikin dan wasa Jardon Sancho, wanda United din take fatan saya a wannan lokacin.

Duk da cewa kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund tana shirin kara bawa dan wasa Jardon Sancho sabon kwantiragi domin ya ci gaba da zama a kungiyar idan har Manchester United ta kasa biyan abinda kungiyar take bukata amma har yanzu United din tana ganin zata iya cimma matsaya da Dortmund.

Manchester United dai ta kai tayin kudin da yakai fam miliyan 89 domin kungiyar ta kasar Jamus ta sallama mata matashin dan wasan dan asalin kasar Ingila mai shekara 20 bayan da kungiyar ta samu tikitin buga gasar cin kofin zakarun turai na shekara mai zuwa.

Tawagar ta Ole Gunner Solkjaer kawo yanzu dai ita ce kawai take zawarcin dan wasan wanda ya koma Dortmund daga kungiyar kwallon kafa ta Manchester City a shekara ta 2017 akan kudi fam miliyan takwas.

Wani rahota daga kasar Jamus ya bayyana cewa dan wasa Sancho ya tabbatar wa da abokan wasansa a kungiyar cewa yana fatan barin kungiyar ta Dortmund bayan da aka kammala kakar wasa ta bana a kasar Jamus kuma a yanzu kungiyar ta fara buga wasannin sada zumunci.

Dan wasan dai ya koma kungiyar Dortmund ne shekaru uku da suka gabata kuma yanzu kungiyar tana neman sama da fam miliyan 100 sai dai dan wasan zai so ya koma kasar Ingila da buga wasa a wannan lokacin .

Wasu rahotanni daga kasar Ingila a kwanakin baya sun bayyana cewa tuni dan wasan ya kammala kulla yarjejeniya da Manchester United akan albashin da zai dinga karba kuma zai saka riga mai lamba bakwai idan har cinikin ya tabbata.

Amma Dortmund tayi fatali da tayin kudi na farko da Manchester United tayi inda kungiyar ta bukaci sama da fam miliyan 100 akan dan wasan duk da cewa abune mai wahala United din ta iya biyan abinda ake bukata daga wajenta.

Sakamakon haka Dortmund ta bayyana cewa zata kara bawa dan wasan sabon kwantiragi domin ya ci gaba da zaman kungiyar idan har Manchester United ba zata iya biyan abinda yakamata ba akan matashin dan wasan.

Manchester United dai tana ganin dan wasan bai kai Fam miliyan 109 ba idan akayi la’akari da yadda cutar Korona ta karya tattalin arzikin duniya ciki har da kwallon kafa ya yinda Dortmund take ganin ba zata rage farashin ba dole sai an biya abinda take bukata kafin ta sayar dashi.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa tuni Manchester United ta fara neman wasu ‘yan wasan idan cinikin Sancho din bai samu ba kuma dan wasan Jubentus Douglas Costa shine wanda kungiyar ta fara Magana dashi sannan kuma a kwanakin baya wakilan United din sunyi Magana da dan wasan Bayern Munchen, Kingsley Coman, wanda shima Solkjaer yake son daukarsa a matsayin aro.

Exit mobile version