Yusuf Shuaibu" />

Har Yanzu Annobar Korona Na Barazana Ga Ayyukan Ababen More Rayuwa – Injiniyoyi

Ababen More Rayuwa

Har yanzu cutar Korona tana barazana wajen kawo tsaiko ga ci gaban ayyukan ababan more rayuwa a cikin fadin kasar nan, saboda mani yawancin ma’aikatan gini ba sa samun tsatuwa wajen komawa aikin yadda ya kamata a wuraren da ayyukan ke gudana. kungiyar injiniyoyi a Nijeriya ita ta bayyana hakan, wanda ta bayyana cewa cutar Korona na ci gaba da kawo tsaiko wajen gudanar da ayyukan ababan more rayuwa a cikin kasar nan.

Sugaban kungiyar Kehinde Osifala, shi ya bayyana hakan a Abuja lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taro shekara-shekara karo na 33.
Ya ce, “Cutar Korona ta yi matukar kawo nakasu ga ci gaban ayyukan ababan more rayuwa a cikin kasar nan. Ana iya gudanar da ayyuka ne lokacin da akwai natsuwa a kan lafiya wanda ma’aikata da masu kulawa da ayyuka za su iya hallara a dukkan wajen da ayyuka ke gudana.”
Ya kara da cewa, nakasun da cutar Korona ta janyowa ga kamfanonin gine-gine abun yana zai iya lissafuwa ba.

Exit mobile version