Daga Khalid Idris Doya,
Biya bayan wani zanga-zangar rufe kan hanyoyi da wasu suka jagoranci yi a wasu sassan karamar hukumar Billiri, Gwamnatin jihar Gombe ya fito balo-balo ta ce har zuwa yanzu dai ba ta sanar da sabon Mai Tangle ba sakamakon cewa har zuwa yanzu ba a kammala tsare-tsaren da suka dace kan lamarin ba.
A wani sanarwar manema labarai da sakataren Gwamnatin jihar Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ya fitar, Gwamnatin ta umarci wadanda suka kulle wasu titina da cewa su gaggauta janyewa nan take.
Sanarwar ta ce da zarar aka kammala bin dukkanin matakan da suka dace, Gwamnatin za ta sanar da sabon tsarkin Tangale.