Har Yanzu Ba Mu Fitar Da Liverpool Ba, Cewar Zidane

Daga Abba Ibrahim Wada

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinadine Zidane, ya bayyana cewa har yanzu basu fitar da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ba daga gasar cin kofin zakarun turai na bana da ake bugawa.
Zidane ya bayyana haka ne a yayinda kungiyarsa take kokarin fafatawa da kungiyar ta kasar Ingila a filin wasa na Anfield a ranar Laraba mai zuwa wasan da shine zakaran gwajin dafi ga kungiyoyin biyu.
Tun bayan da hukumar kula a kwallon kafa ta nahiyar turai ta fitar da jadawalin yadda za’a ci gaba da buga wasannin cin kofin zakaru na nahiyar turai aka kuma hada Liverpool da Real Madrid aka fara bayyana yadda wasannin zasu kasance ganin cewa Liverpool din a wannan yanayin bata buga abin azo a gani.
A wasan farko da kungiyoyin suka fafata Real Madrid ce ta samu nasara da ci 3-1 a kasar Sipaniya, dan wasa binicius ne ya zura kwallaye biyu sannan kuma Marco Asensio ya zura kwallo daya ya yinda Muhammad Salah ne ya ci wa Liverpool kwallonta guda daya.
Shima mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinadine Zidane, ya bayyana cewa kungiyar Liverpool zata fito da karfinta a wasan da kungiyoyin biyu zasu fafata da juna a kasar Ingila a ranar Laraba.
Real Madrid za ta fafata da Liverpool a wasan dab da na kusa da na karshe na Champions League sai kungiyar Manchester City za ta buga nata wasan da kungiyar Borussia Dortmund a wasa na biyu a kasar Jamus
Ya yin da Chelsea za ta barje gumi da FC Porto bayan da kungiyar ta kasar Ingila ta zura kwallaye biyu a ragar Porto a wasan farko da suka fafata a gidan kungiyar ta kasar Portugal wato FC Porto.
Mai rike da kofin Bayern Munich za ta buga wasanta na biyu da Paris St-German wato kungiyar da suka buga wasan karshe na gasar a bara wasan da ake ganin ko dai ayi ramuwa ko kuma a sake maimaita abinda ya faru a baya a kasar Jamus.
Za a ci gaba da buga wasannin biyun farko na gasar Champions League a ranar 14 da 15 ga watan Afrilun nan da muke ciki  sannan za kuma a buga wasannin zagayen farko na kusa da na karshe a gasar a ranakun 27 da 28 ga watan Afrilu ya yin da za a buga wasannin zagaye na biyu a ranakun 4 da 5 ga watan Mayu.
Liverpool da Real Madrid sun fafata a wasan karshe na gasar a shekarar 2018 inda Real Madrid, wadda ta lashe kofin sau 13, ta yi nasara a wasan da ci 3-1 sai dai duka kungiyoyin biyu sun fafata da juna sau shida a gasannin turai, kuma ko wacce ta samu nasara a wasanni uku ciki har da wanda Liverpool ta yi nasara da ci 1-0 a wasan karshe na shekarar 1981.
Sau daya Manchester City da ke jan ragamar gasar Premier ta hadu da kungiyar Dortmund ne sau daya kawai a matakin rukuni a gasar, inda ta yi 1-1 da sannan kuma ta yi rashin nasara da 1-0 a shekarar 2012.
Sau takwas Chelsea ta yi wasa da FC Porto, ta yi nasara sau biyar ta kuma yi rashin nasara sau biyu, ta cire kungiyar ta Portugal 3-2 a zagaye sili daya kwale a zagayen ‘yan 16 a kakar wasa ta 2007.
kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ko Paris St-Germain daya za ta fafata da Manchester City ko Borussia Dortmund ya yinda Real Madrid ko Liverpool daya za ta fafata da Porto ko Chelsea.

Exit mobile version