Daga Abba Ibrahim Wada
Kocin Barcelona Ernesto Valverde, ya ce Lionel Messi zai ci gaba da amsa sunansa na fitaccen dan wasa a duniya ko ya lashe kyautar dan ƙwallon duniya ta bana ko bai lashe ba.
A farkon watan nan ne mujallar kwallon kafa ta Faransa ta fitar da sunayen fitatttun ‘yan wasan, inda mutane da dama suka yi amannar cewa Cristiano Ronaldo na Real Madrid zai iya lashe kyautar.
Ko da yake kocin ya gamsu cewa Messi ba ya bukatar wata kyauta da za ta nuna shi ne fitaccen dan wasa a duniya.
Ɓalɓerde yace, messi babban dan ƙwallo ne kuma har yanzu babu kamarsa kowa yasan haka, kuma idan ana maganar babban dan wasa messi ake Magana.