Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Karim Benzema, ya bayyana cewa yadda ake ci gaba da buga gasar La liga ta bana babu kungiyar da zata iya cewa itace zata lashe gasar.
Benzema ya bayyana haka ne bayan Real Madrid ta tsallake rijiya da baya, a gasar La Liga ta Spain yayin wasan da suka fafata da Atletico Madrid, wanda suka tashi kunnen doki 1-1 a wasan hamayyar birnin Madrid
Tsohon dan wasan Barcelona Luis Suarez ne ya fara ci wa Atletico Madrid kwallo kafin kaiwa ga tsakiyar zangon farko na mintuna 45, ana gaf da karkare wasan ne kuma Karim Benzema ya ramawa Real Madrid.
Sai dai sakamakon wasan ya baiwa Barcelona damar matsawa kusa da Atletico Madrid da a yanzu haka take jagorantar gasar La Liga da maki 59 bayan nasarar da ta samu akan Osasuna da 2-0 a karshen mako, a yanzu Barcelona ke matsayi na biyu da maki 56, yayin da Real Madrid ke biye da ita a matsayi na uku da maki 54.
“Tabbas wasannin wannan shekarar basa yiwa kowacce kungiya dadi duba da irin yadda aka samu matsaloli musamman na rashin ‘yan kallo sannan kuma ‘yan wasa suna gajiya ga yawan jin ciwo saboda haka abune mai wahala a samu wanda zai lashe gasar har sai ranar wasan karshe” in ji Benzema