Abba Ibrahim Wada" />

Har Yanzu Bamu Gama Aiki Akan PSG Ba – Cristiano

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Cristiano Ronaldo, ya bayyana cewa har yanzu akwai aiki a gabansu a wasan da suka buga da kungiyar Paris Saint German, inda ya ce suna bukatar gama aikinsu a kasar faransa idan sun je.

Ronaldo ya bayyana haka ne bayan da kungiyarsa ta doke kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint da ci 3-1 a filin wasa na Santiago Barnabue.

Dan wasan ya ce duk da cewa sun samu nasara da kwallaye uku, amma har yanzu akwai ragowar aiki domin akwai ragowar minti 90 a kasar faransa kuma suna bukatar dagewa don tabbatar da cewa sun nuna su ne Real Madrid.

Ya ci gaba da cewa PSG babbar kungiya ce, kuma suna da manyan ‘yan wasan gaba wadanda suna da hatsari sosai. sai dai ya ce hakan baya nufin ba za su iya doke su ba, saboda su ma Real Madrid babbar kungiya ce wadda take da shahararrun ‘yan wasa.

Ya kara da cewa ‘yan wasan kungiyar sun buga abinda ya kamata, kuma sannan magoya baya sun nuna masu goyon baya yadda ya kamata kuma suna godiya sosai kuma za su cigaba da farantawa magoya bayan kungiyar rai sosai.

A ranar 6 ga watan Maris mai kamawa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid za ta kai ziyara kasar Fransa, domin fafatawa a wasa na biyu na gasar wanda PSG din za ta barbi bakunci.

Exit mobile version