Manajan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya yi ikirarin cewa har yanzu bai karaya da cewa kungiyar tasa za ta iya wuce takwararta Manchester City tare da dage kofin firimiya a bana ba.
A cewar Klopp ya na da kwarin gwiwar cewa Liberpool cikin wannan kaka za ta kafa tarihin dage kofuna 3 ko fiye ciki kuwa har da na firimiya da kuma zakarun Turai da ta samu damar zuwa wasan karshe.
Manchester City ta tsawaita tazarar da ke tsakaninta da Liberpool daga maki daya zuwa 3 bayan lallasa Newcastle da kwallaye 5 da nema wanda ya bata damar zarta ta hatta da yawan kwallaye kwana guda bayan Reds ta yi canjaras da Tottenham da kwallo daya da daya.
Jurgen Klopp ya bayyana cewa duk da yana fatan shigewa gaban Manchester City don lashe kofin firimiya hakan ba zai hana shi tattala ‘yan wasansa don tunkarar wasannin karshe na cin kofin FA tsakaninsu da Chelsea a asabar din nan mai zuwa ba da kuma wasan karshe na cin kofin zakarun turai ranar 28 ga watan nan tsakaninsu da Real Madrid.
A cewar Klopp idan har ba a kai ga wasan karshe ba Liberpool ba za ta cire rai kan yiwuwar dage kofin ba, kalaman da ke zuwa dai dai lokacin da Pep Guardiola na Manchester City ke ikirarin cewa ilahirin Ingila na goyon bayan Liberpool ne don ganin ta lashe firimiya.