Har Yanzu Ban Hakura Da Lashe Gasar Firimiya Ba –Solkjaer

Firimiya

Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Ole Gunner Solkjaer, ya bayyana cewa har yanzu yana da yakinin cewa kungiyarsa zata lashe gasar firimiyar Ingila duk da tazarar maki 10 dake tsakaninsa da Manchester City.

A daren ranar Lahadi ne Manchester United ta doke kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United da ci 3-1 a wasan mako na 25 a gasar Premier League ranar Lahadi a babban filin wasa na Old Trafford.

Dan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford ne ya fara ci wa kungiyar kwallon tun kafin a tafi hutun rabin lokaci, yayin da Newcastle ta farke ta hannun Saint-Madimin minti shida tsakani.

Bayan da kungiyoyin suka yi hutu suka koma karawar zagaye na biyu ne dan wasa Daniel James ya karawa Manchester United kwallon ta ta biyu, sannan sai Bruno Fernandes ya ci ta uku a bugun fenariti.

Wannan ne wasa na 10 da aka doke kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United a Premier League da hakan ya sa ta koma ta hudun karshe da tazarar maki uku tsakaninta da Fulham ta ukun karshe a teburin bana.

Ita kuwa Manchester United wadda ta koma ta biyu ta zararar maki 10 tsakaninta da Manchester City ta ci wasa na biyu kenan a Lig a fafatawa shida, bayan canjaras da West Brom a karshen mako.

Manchester United za ta ziyarci kungiyar kwallon kafa ta Chelsea a karawar Premier ranar 28 ga watan Fabrairu, ita kuwa Newcastle za ta karbi bakuncin Wolberhampton ranar 27 ga watan na Fabrairu.

Sai dai kafin wasan na Manchester United da Chelsea tawagar ta Ole Gunner Solkjaer zata karbi bakuncin kungiyar kwallon kafa ta Real Soceidad a wasa na biyu na gasar cin kofin Europa a filin wasa na Old Trafford a wasan farko dai a gidan Soceidad United ce ta samu nasara da ci 4-0

 

Exit mobile version