Har Yanzu Korona Na Cin Rayuka – Kwamishinan Muhalli Na Abiya

Rayuka

Daga KALU EZIYI, Umuahia

 

Kwamishinan muhalli na jihar Abiya, Tony Nwanmuo ya gargadi mazauna jihar cewa har yanzu cutar korona na ci gaba da yaduwa kuma ya shawarce su da su ci gaba da daukar matakan kare kai daga cutar ta duniya.

Ya ci gaba da cewa, ba za dauki rahoton ragin da aka ba da na kamuwa da cutar ta Corona a matsayin wata alama ta kawar da ita ba, amma dukkan wannan ya biyo baya ne saboda bin ka’idojin rigakafin da mutane ke yi.

Nwanmuo ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da LEADERSHIP a Umuahia, babban birnin jihar, bayan sanya idanu kan aikin tsabtace muhalli da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata a jihar, yana mai cewa har yanzu kwayar ta na shafar mutane a duniya.

Wanda ya samu wakilcin daraktan kula da gurbatar muhalli da lafiyar muhalli a ma’aikatar, Ikechukwu Ukaegbu, ya jaddada cewa ya kamata su yi kokarin tsabtace muhallinsu a kai a kai.

Ya kara da cewa, “Har yanzu cutar ba ta kare ba. Har yanzu muna yin taka tsan-tsan da mu’amala da junanmu. Muna kuma samun raguwar kamuwa da cutar a cikin jihar, wanda hakan ya bai wa mutane damar sakin jiki. Ma’aikatar ta kasance tana gayawa mutane cewa kada su saki jiki. Ya kamata ko dai su wanke ko kuma tsabtace hannayensu a kai a kai, su kiyaye nisantar jama’a kamar yadda ya kamata, kuma su kiyaye da sauran abubuwan kiyayewa” in ji shi.

“Da yake nuna farin cikinsa da gudanar da atisayen, ya bayyana damuwar sa na cewa wasu mazauna yankin musamman matasa sun ci gaba da amfani da lokacin don ko dai su yi wasan kwallon kafa a kan hanyoyi ko kuma yin sauran wasanni.”

Kwamishinan, wanda ya ci gaba da cewa ma’aikatar ba za ta kara amincewa da irin wannan dabi’ar ba, ya bayyana cewa wadanda ke kan mahimman ayyuka ne kawai aka ba su izinin motsawa yayin motsa jiki na awanni biyu.

Nwanmuo ya kuma nuna rashin jin dadinsa na cewa, duk da kiraye-kirayen da ma’aikatar ke yi na kin zubar da shara a magudanan ruwa wanda ya ce yana haifar da ambaliyar ruwa da zaizayar kasa, har yanzu wasu gidajen ba su saurari sakon ba. A cewarsa, ma’aikatar a nata bangaren za ta ci gaba da tabbatar da tsaftar muhalli na jihar tare da yin kira ga mazauna yankin da su hada hannu da ita a wannan hanyar don amfanin kowa.

 

Exit mobile version