Abba Ibrahim Wada" />

Har Yanzu Kwararru Na Fatan A Sallami Kociyan Super Eagles

Kociyan Super Eagles

Masana harkar kwallo kafa a Najeriya na ci gaba da nuna bukatar ganin anyi waje da mai horar da ‘yan wasan tawagar kwallon kafar kasar nan Super Eagles, Genot Rohr, sakamakon rashin tabuka abin arziki a wasannin da kasar nan ta buga a ‘yan kwanakin nan.

Na baya-bayan nan da yayi tsokaci shine, Tsohon dan wasan kasar Jonathan Akpoborie, wanda ya ce kocin na Super Eagles dan kasar Jamus bai cancanci sabunta kwantiraginsa ba sakamakon rawar da kungiyar ke takawa karkashinsa yanzu haka, masamman abin da ya faru a wasan da suka buga a jihar Edo, a neman cancantar shiga gasar cin kofin Afirka.

A watan Mayu ne Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta bai wa Rohr sabon kwantaragin shekaru biyu wanda zai kai shi har zuwa shekarar 2022, a matsayin koci mafi tsawo a tarihin kasar nan tun farkon fara fafatawar Nigeriya a wasannin duniya.

Akpoborie ya yi amannar cewa Rohr ya zama tamakar wani nauyi ga kungiyar ta super Eagles, bayan kunnen doki da suka yi da Saliyo da ci 4 da 4 sannan kuma da wasa na biyu da suka fafata aka tashi 0-0

Shima ministan matasa da bunkasa wasanni na kasar nan, Sunday Dare ya bayyana alamun yiwuwar sallamar kocin babbar tawagar kwallon kafar kasar nan ta Super Eagles bayan wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Afrika da Saliyo.

Minister Sunday Dare ya bayyana takaicinsa dangane da irin wannan rikitowa da Super Eagles suka yi, kana ya bukaci martani mai gauni daga gunsu a wasannin da za suyi nan gaba na neman shiga kofin na Africa.

Sai dai ya ki cewa komai a game da dacewa ko rashin dacewar Gernot Rohr a matsayin kocin tawagar, inda yake cewa abin dake gabansu shine samun tikitin zuwa gasar cin kofin Afrika wanda za’a buga a shekara mai zuwa.

Ministan  ya ce za su nazarci aikin Rohr don tantancewa ko shine ya dace ya ci gaba da horar da ‘yan wasan Najeriya kuma idan suka fahimci ba zai iya kai kasar nan inda ake fata ba zasu sallame shi domin bawa wanda ya cancanta.

Sai dai a nasa bangaren tsohon dan wasan tawagar Super Eagles ta Nigeriya, Garba Lawal, ya bayyana cewa bai kamata a halin da ake ciki ba a kori mai koyar da tawagar ‘yan wasan Super Eagles ta Nigeriya, Gernot Rohr, saboda lokaci ya kure.

“Tabbas anyi kuskure a wasan farko da aka fafata da kasar Saliyo saboda bai kamata ‘yan wasa kamar na Nigeriya su zura kwallaye hudu ba amma a farke gaba daya wannan ya nuna rashin kishi da mayar da hankali” in ji Garba Lawal

Ya kara da cewa “Amma kuma bai kamata a kori mai koyarwa a irin wannan lokacin ba saboda saura wasanni biyu a kammala wasannin neman cancantar kuma har yanzu Nigeriya ce akan gaba acikin rukunin sannan zasu samu tikitin idan suka samu nasara a wasa daya nan gaba”

Sai dai wata majiya daga hokumar kwallon kafa ta kasa ta bayyana cewa shugabannin hukumar basu da niyyar korar mai koyarwa Gernot Rohr sai dai sun gargade shi akan dole ne sakamakon wasanni ya canja a nan gaba idan yanason ya ci gaba da koyar da tawagar ta Super Eagles har zuwa gasar cin kofin nahiyar Africa da kuma gasar cin kofin duniya a shekarar 2022 da kasar Katar zata karbi bakunci.

Exit mobile version