Har Yanzu Manchester United Ba Ta Hakura Da Trippier Ba

Trippier

Wasu rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United bata hakura da sayan dan wasa Kieran Trippier ba duk da cewa kungiyar da dan wasan yake bugawa wasa, Atletico Madrid ta bayyana cewa dan wasan zaiyi tsada.

Kungiyar Manchester United dai na fatan daukar dan kwallon tawagar kasar Ingila mai buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, Kieran Trippier amma farashin fam miliyan 43 ya yi mata tsada.

Tsohon dan wasan na Burnley da Manchester City mai tsaron baya, ya lashe kofin La Liga a kakar da aka kammala, bayan da ya koma kungiyar daga Tottenham akan farashin fam miliyan sha biyar.

Dan wasan mai shekara 30 na son komawa Manchester United kuma kusa da iyalinsa da ke Arewa maso yamma da Ingila, watakila ya nemi izinin barin Sifaniya sannan kocin Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer ya hangi barakar da Trippier zai toshe da rawar da zai taka a kungiyar.

Trippier ya tsare bayan Ingila daga hagu a gasar cin kofin nahiyar Turai da ta doke Croatia ranar Lahadi kuma Manchester United ba ta da niyyar sayen dan kwallon kamar yadda Atletico Madrid ta yi masa farashi, saboda yawan shekarunsa kuma saura kakar wasa daya yarjejeniyarsa ta kare a Atletico Madrid din.

Kudin da kungiyar ta Sifaniya ta gindaya wa Tripper ya kai fam miliyan 34 ga duk wadda ke son daukar mai tsaron bayan ko da kwantiraginsa bai kare ba sai dai hakan zai hana Manchester United zawarcinsa saboda kudin yayi musu yawa.

Kociyan Manchester United, Ole Gunner Solkjaer dai yana fatan sayan dan wasa Trippier domin ya yiwa Aaron Wan-Bissaka kishiya a bangaren dama na baya duk da cewa dan wasan wanda shima dan Ingila ne yana buga abinda yakamata.

Exit mobile version