Har Yanzu Manchester United Tana Neman Maguire

Har yanzu kungiyar kwallon kafa ta Manchester United tana zawarcin dan wasan baya na kungiyar Leceister City, Harry Maguire, duk da cewa ta kai tayin farko na fam miliyan 70 kuma kungiyar Leceister City din tayi fatali da tayin kudin.

Tun farkon kammala kakar wasan data gabata aka fara danganta Manchester United da neman matashin dan wasan bayan dan asalin kasar Ingila sai dai kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ma ta shiga zawarcin dan wasan bayan da dan wasanta na baya Bicent Kompany ya bar kungiyar.

Da farko Leceister City tayi wa dan wasan farashi na fam miliyan 70 sai dai daga baya data fahimci kungiyoyin biyu na Manchester United da City suna zawarcin dan wasan sai suka kara masa kudi inda suka ce sai an biya fam miliayn 90 ga duk kungiyar da take son sayansa

Sai dai wata majiya ta tabbatar da cewa duk da cewa Leceister City tayi fatali da tayin farko na Manchester United amma har yanzu United din bata hakura da neman dan wasan ba kuma zata kara taya dan wasan da farashin da kungiyar takeso.

Tuni dai Manchester United ta sayi ‘yan wasa guda biyu, Daniel James, daga kungiyar kwallon kafa ta Swansea City da kuma Aaron Wan-Bissaka daga kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace akan kudi fam milyuan 50.

Har ila yau, Manchester United tana cigaba da zawarcin dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Lazio, Sergej Milenkobic-Sabic wanda akayiwa farashi fam miluyan 90 sai kuma dan wasa Bruno Fernandez na kungiyar Sporting Lisbon ta kasar Portugal wanda shima United din ta dade tana nema.

Exit mobile version