Yusuf Shuaibu">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home TATTALIN ARZIKI

Har Yanzu Masana’antun Nijeriya Na Fafutukar Farfadowa — Kungiyar MAN

by Yusuf Shuaibu
February 1, 2021
in TATTALIN ARZIKI
2 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Duk kokarin tsamo ‘yan Nijeriya daga kangin talauci wajen neman samar da damarmakin ayyukan yi lokacin da samu wadatar kudade, shugaban kungiyan masana’antun Nijeriya (MAN),Mansur Ahmed ya bayyana cewa, bangaren masana’antu a yanzu haka hana farfadiya. A cikin binciken da aka gabatar, kididdigar yawan masu masana’antu ya nuna cewa an samu kowa baya mai matukar yawa a wannan shekarar sakamakon matsin tattalin arziki da kasar nan ta shiga.

Ahmed ya bayyana hakan ne a wajen taron manema labarai wanda ya gabata a jiya. Ya bayyana cewa, daga cikin manyan matsalolin da bangaren masana’antu ke fuskanta a yanzu sun hada da wahalar samun canjin kudaden kasar waje domin sayo kayayyakin da za a sarrafa wanda babu su a cikin gida Nijeriya da tsadar farashin wutar lantarki da kuma tsadar kudaden sufuri. Sauran sun hada da karancin masu bukatar kayayyaki da waahalar samun kudade da matsinlamba daga wajen hukumomin gwamnati da rashin kyawan gudanarwa da rashin kayayyakin da za a sarrafa da rashin manufofi masu kyau da dai sauran su. Ya kara da cewa, wadannan matsaloli su suka hana ci gaban bangaren masana’antu, wanda fannin ne da zai samar da ayyukan yi masu yawa da kuma kudade ga kasar nan. Ya yaba wa gwamnatin tarayya bisa sake bude iyakokin kasar nan domin gudanar da harkokin kasuwanci musamman ma a harkokin kasuwancin da ke gudana a tsakanin mutanen Afirka. Ya ce, kasuwancin yana gina kasashen Afirka wajen canjin kayayyakin da aka sana’anta a tsakanin tattalin arzikin ‘yan Afirka wanda yake bai wa Afirka karfi a bangaren tattalin arziki a duniya.
“Ina farin cikin da wannan samun daman a ci gaba ga kowacce kasa wajen gudanar da yarjejeniya da hada kai domin samun nasara. Amma kuma hakan ba zai taba kasancewa ba sai an fuskanta wasu matsaloli,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa, an fara samun raguwar matsalolin da bangaren masana’antu ke fuskanta. Ya bayar da shawara a hada hannu da karfe wajen dakile wadannan matsaloli da suka addabi fannin. Ya ce, akwai bukatar kasashen su tabbatar da shugabancin da kowa zai amince domin samun nasara mai daurewa. Ya ce, bambamcin da za a samu dai shi ne, wasu kasashe za su tabbatar da kulawa ga duk wata dokokin da aka zantar, yayin da wasu kuma za su yi burus da dokokin, wanda da haka ne muke kira a saka ido sasai a dukkan yankunan daomin tabbatar da kasashen sun yi abin da ya dace.”
Ya ce, kungiyar MAN ta gudanar da mabambamtan taron karawa juna sani ga mambobinta domin samun alfanu a cikin wannan yarjejeniya tare da fatan gwamnatin Nijeriya za ta taka rawar gani a wannan bangare, domin samun damar cin moriyar yarjejeniyar harkokin kasuwanci. Ya kara da cewa, wajibi ne ga hukumomin da ke kulawa da tattalin arziki da su dauki matakai wajen samun nasarar ci gaban tattalin arziki a cikin gida da kuma na kasa da kasa.

SendShareTweetShare
Previous Post

Muna Da Matsalar Zura Kwallo A Raga – Solkjaer

Next Post

Babu ’Yar Rufa-rufa A Kasafin Kudin 2021 – Buhari

RelatedPosts

Emefiele

Bunkasa Tattalin Arziki: Nijeriya Na Bukatar Kara Kaimi Wajen Adana Abinci – Emefiele

by Yusuf Shuaibu
1 day ago
0

Daga Mahdi M. Muhammad   Gwamnan Babban bankin Nijeriya (CBN),...

Bankuna

Rahoton Bangaren Bankuna Yana Nuna Samun Cigaba Mai Matukar Ma’ana – CBN

by Yusuf Shuaibu
1 day ago
0

Daga Mahdi M. Muhammad   Rahoton karshe na Babban bankin...

Gwamnatin Masar

Lantarki: Nijeriya Za Ta Hada Kai Da Masar

by Yusuf Shuaibu
1 day ago
0

Daga Mahdi M. Muhammad   Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya...

Next Post
Babu ’Yar Rufa-rufa A Kasafin Kudin 2021 – Buhari

Babu ’Yar Rufa-rufa A Kasafin Kudin 2021 – Buhari

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version