Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Har Yanzu Masu Rajin Kare Hakkin Dan Adam Na Amurka Ba Su Ji Kunya Ba?

Published

on

Kwanan baya, kungiyar kare hakkin jama’a ta kasar Amurka wato ACLU ta aika wata wa kwamitin kula da hakkin dan Adam na MDD wasika, inda a cikinta ta bayyana cewa, lokaci ya yi da za a gudanar da bincike tare da yanke hukunci kan Amurka, kamar yadda ta yi wa sauran kasashe. Cikin wasikar, kungiyar ta kuma bukaci MDD da ta shirya taron gaggawa kan yadda ‘yan sandan Amurka suka gallazawa masu zanga-zanga tare da bin bahasin batutuwa masu alaka da haka, ta kuma jaddada cewa, tilas ne MDD ta martaba bukatun al’ummar Amurka da kuma dora wa gwamnatin Amurka laifin keta hakkin dan Adam.

Cikin kwanaki 10 da suka gabata, mutuwar wani Ba’amurke bakar fata mai suna George Floyd ta haifar da gagarumar zanga-zangar neman kare hakkin dan Adam a Amurka baki daya. Amma abin bakin ciki shi ne wasu ’yan siyasan Amurka da kafofin yada labaru ba su yi nadaman faruwar lamarin ba, maimakon haka ma, sai suka ci gaba da rura wutar rikicin wariyar al’umma, wanda yake illata hadin kan al’ummomin Amurka.
Abun da yake faruwa a Amurka ya sake sanya kasashen duniya kara sanin cewa, wadancan ’yan siyasan Amurka da kullum suke kiran kansu masu rajin kare hakkin dan Adam su ne wadanda suka haifar da matsalar hakkin dan Adam. A matsayinsa na babban jakadan Amurka, sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo ya kan fake da sunan “demokiradiya da hakkin dan-Adam” yana sokar wasu kasashe, amma bai ce kome ba kan zanga-zangar kin amincewa da wariyar al’umma dake faruwa a cikin gida Amurka ba.
Yanzu kowa ya san cewa, ainihin tunanin wasu ’yan siyasan Amurka dangane da kiyaye hakkin dan Adam shi ne keta hakkin dan Adam don biyan bukatunsu. Shin wadancan masu rajin kare hakkin dan Adam ba su ji kunyar fadan “’yanci” da “dimokuradiyya”? Lokaci ya yi da za a kawo karshen nuna fuska biyu kan batun kiyaye hakkin dan Adam. (Mai FassarawaTasallah Yuan)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: