Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta doke kungiyar Real Soceidad da ci 2-1 a wasan gasar Laligar da kungiyoyin biyu suka fafata a wasan mako na 19 bayan da ranar Litinin aka kammala wasannin mako na 13 a gasar kasar ta Spaniya.
Kyaftin din Barcelona, Lionel Messi yana cikin ‘yan wasa 22 da Ronald Koeman ya bayyana da za su kara a filin wasa na Camp Nou kuma Messi wanda shi ne kyaftin din Argentina, da ace ya zura kwallo a raga to zai yi kan-kan-kan ko goge tarihin da Pele ya kafa wajen cin kwallaye a fagen kwallon kafa a kungiya daya.
Pele tsohon zakaran Brazil ya ci kwallo 643 a kakar wasa 19 da ya yi a tsohuwar kungiyarsa ta Santos, kuma shi ne wanda ya ci kwallaye da yawa a kungiya daya, bajintar da ya kafa kusan shekara 50.
Messi ya ci Sociedad kwallo 14
Duk da cewa a wasan na ranar Laraba dan wasa Messi bai zura kwallo a raga ba amma a baya ya ci Real Sociedad kwallo 14 a wasanni 21 da ya fuskanci kungiyar a tarhin kwallonsa kuma kafin bullar cutar korona, Messi ya ci Sociedad kwallo a karawar da Barcelona ta yi nasara da ci 1-0 cikin watan Maris.
Wasan da Barcelona ta buga da Sociedad ya bai wa Messi damar kan-kan-kan da Pele wajen cin kwallaye a kungiya daya haka kuma ya samu damar zama na daya a cin kwallaye a gasar La Liga ta shekarar nan, kuma nasarar za ta bai wa kungiyar yin sama a teburin La Liga sai dai Messi bai zura kwallo a raga amma kuma kwallayen Dabid Alba da Frankie De Jong sune suka bawa Barcelona nasara a fafatawar..
Karawar da kungiyoyin biyu sukayi ita ce ta mako na 19 da ya kamata su yi, amma za su buga wasan, bayan kammala gumurzun mako na 13 ranar Litinin sai dai Real Sociedad ce ke jan ragamar teburin La Liga da maki 26, bayan buga wasanni 13 da nasara bakwai da canjars biyar aka doke ta wasa biyu a kakar bana.
Barcelona tana mataki na takwas a teburi da maki 20, bayan buga wasa 12 da yin nasara shida da canjaras biyu aka doke ta fafatawa hudu sannan kungiyar Atletico Madrid ce ta biyu da maki 26 iri daya da na Sociedad, sai dai kungiyar birnin Madrid tana da kwantan wasa biyu.
Real Sociedad ta ci kwallo 23 a raga a kakar bana, ita kuwa Atletico 21 ta ci, dalilin da ya sa kungiyar ta dare teburin La Liga sannan kuma Barcelona ta yi nasarar doke Lebante da ci 1-0 a wasan mako na 13 kafin wasan na Laraba , ita kuwa Sociedad tashi ta yi 1-1 da Eibar ranar Lahadin data wuce.
Sauran sun hada da Coutinho da Lenglet da Pedri da Trincco da Jordi Alba da Matheus da F. De Jong da Umtiti da Inaki Pena da O. Mingueza da kuma Konrad sai kuma wadanda ke jinya sun hada da Pikue da Dembele da Sergi Roberto da kuma Ansu Fati.
Shi kuwa Junior Firpo baya cikin ‘yan wasan Barca, bayan da aka amince ya yi hutu kan matsalar ta radin kansa bugu da kari a ranar Litinin aka raba jadawalin gasar Champions League karawar zagaye na biyu ta kungiyoyi 16 da suka rage a wasannin.
Kuma Barcelona za ta karbi bakuncin Paris Germain a wasan zagayen farko a Camp Nou da za su kara cikin watan Fabrairu, daga nan su buga wasa na biyu cikin watan Maris a Faransa ita kuwa Sociedad tana buga Europa League za kuma ta fafata da Manchester United wadda ta bar buga Champions League.
Tun kafin buga wasan daman Real Sociedad ta kwan da sanin kalubalen da ke gabanta a Camp Nou, kuma rabon da Barcelona ba ta yi nasara ba a irin wannan hacuwar tun 1-1 da suka buga a La Liga ranar 27 ga watan Nuwamba 2016.
Sai da Barcelona na fuskantar kalubale a bana, inda kwanan nan Cadiz ta doke ta 1-0 a La Liga da rashin nasara da ta yi a hannun Jubentus da ci 3-0 a Champions League a Camp Nou amma kuma doke Lebente da Barcelona ta yi a karshen mako ya kara mata kwarin gwiwar samun nasara akan Sociedad.
Wadanda suke kan gaba a cin kwallaye a La Liga:
Iago Aspas Celta de Bigo7
Mikel Oyarzabal Real Sociedad7
Carlos Soler Balencia 5
Paco Alcacer Billarreal 5
Cristian Portugues Real Sociedad 4
Manu Ballejo Balencia C.F 4
Jose Luis Morales Lebante 4
Ansu Fati Barcelona 4
Marcos Llorente Atletico Madrid 4
Cristian Tello Real Betis 4
Karim Benzema Real Madrid 4
Angel Getafe CF4