Duk da cewa wasu suna ganin Cristiano Ronaldo shi ne silar matsalolin kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ko kuwa shi ne maganin matsalolin kungiyar, wannan ita ce tambayar da ake ta yi a kungiyar.
Kwallaye uku masu ban-mamaki da Ronaldo ya zura a ragar kungiyar kwallon kafa ta Norwich City a ranar Asabar din da ta gabata sune suka bai wa kungiyar kwarin gwiwar samun gurbi a Gasar Zakarun Turai ta kaka mai zuwa.
Rawar da ya taka ta sa dan kasar ta Portugal ya kai ga zura kwallaye 99 a gasar firimiya sannan ya zama na uku, da hadin gwiwar wasu ‘yan wasan, a matsayin wanda ya fi zura kwallo a gasar firimiya ta bana inda ya ci kwallo 15.
Wannan ita ce kaka ta 16 a jere da Ronaldo ya ci kwallo 20 zuwa sama a dukkan gasa, kuma ya zarta kowanne dan wasan Manchester United da kwallo 12 a bana sannan wadannan alkaluma ne da za su sa mutane su yi ta magana kan dan wasan mai shekara 37? Kamar yadda kocin Norwich Dean Smith ya tabbatar.
Abin da hakan ke nufi shi ne, idan dai Ronaldo zai ci gaba da zura kwallaye, bai kamata Manchester United ta raba-gari da shi ba kuma a halin yanzu, kwallayen da yake zurawa su ne suke fitar da kungiyar daga kunya. Idan aka hada da kwallo uku da ya ci a karawarsu da Tottenham wasanni biyu da suka gabata, Ronaldo ne dan wasan daya tilo da ya zura wa United kwallaye a Gasar Firimiya da aka saka shi a ciki tun wasan da suka doke Leeds ranar 20 ga watan Fabrairu.
Zai ci gaba da zama mai muhimmanci ga tawagar United, kuma idan Erik ten Hag ya zama kocin kungiyar kamar yadda aka yi hasashe, dole a tattauna kan ko Ronaldo zai ci gaba da zama a Old Trafford a shekarar karshe ta kwangilarsa.