Shugaban kungiyar matasan jihar Sokoto kuma dan gwagwarmayar ganin an samar da ingantacciyar gwamnati, Umar Abdullahi Lili ya bayyana cewa tun bayan zaben 2015 babu wani romon dinokradiyya da ake sharba a jihar Sokoto, illa mulkin daga kai sai ‘ya’yanka.
Lili wanda ya bayyana hakan a hirar sa da manema labarai, ya kara da cewa duk da ikrarin da gwamnatin Tambuwal take yi na cewa an dakile harkar ta’addanci, ba a taba lokacin da ake harkar ta’addanci a jihar Sokoto ba irin yanzu, saboda yanzu ne ake kashe mutane kamar kaji ba tare da an dauki mataki ba.
Ya ce ko makonni biyu ba a yi ba a cikin karamar hukumar Sokoto ta Arewa an dabawa wasu mutane biyu wuka kuma ba a dauki mataki ba, saboda ‘ya’yan jam’iyyar gwamnati mai ci ne suka aikata laifin.
Matashin ya kara da cewa salon mulkin dimokradiyyar Nijeriya ba shi da maraba da mulkin mallaka domin ba a iya bambance mulkin soja ake yi ko kuma na dimokadiyya.
A cewar sa gwamnatin tarayya ko ta jiha ba ta barin mutane su fadi albarkacin bakin su, wanda hakan ya sa mutane suke tsoron dauri ko wani abu makamancin haka.
Ya ce a matsayinsa na Basakkwace ba a yi shi don tsoro ba don haka ne ya fito ya fadi gaskiya komai dacinta.
Ya kara da cewa a farkon mulkin dimokradiyya a 1999 Attahiru Bafarawa ya yi iya kokarin sa kuma jama’a ma sun shaida. Daga bisani ya mikawa Aliyu Wamakko, wanda ko makiyin Allah ya san cewa Wamakko ya taka rawar gani a fadin jihar Sokoto.
“A wannan gwamnati ta Tambuwal babu wani muhimmi aiki da za a nuna a ce an yi wa mutanen Sokoto, kullum sai yawo da takarda.
Lili ya ci gaba da cewa duk Nijeriya babu inda harkar ilmi da sauran al’amuran ci gaban dan Adam suka tabarbare kamar jihar Sokoto. Domin a cewar sa kafin bulluwar cutar corona idan mutum ya je makarantun Sokoto ya ga halin da yara dalibai suke ciki sai ya zubar da hawaye. Saboda babu kujeru, babu kulawa har ta kai ga sai yara sai sun karbo kudi a wurin iyayensu ake siya musu allin rubutu.
“Idan ka je makarantun jihar Sokoto za ka ga babu kofofi, babu tagogi kuma duk girman makaranta sai ka je ka tarar da malami daya yana koyawa yara darasi”, cewar Lili.
Lili ya kara da cewa don haka batun cewa Gwamna Tambuwal ya ce ya kashe bilyoyin kudi a fannin ilmi ba gaskiya ba ne, ya fadi hakan ne kawai domin ya burge ‘yan jarida. Domin su al’ummar jihar Sokoto suna sane da cewa babu wani aiki da aka yi na milyan dubu.
“Sannan kuma batun cewa an samar da kujerun makaranta sama da dubu dari biyu ba gaskiya ba ne, saidai idan a cikin gidansa gwamnan ya zuba kujerun.
“Ni da kaina na ziyarci makarantun, wasu makarantun ma da hawaye na dawo saboda yadda aka banzantar da su”, cewar Umar Lili.
Umar Lili ya kara da cewa batun zaftare wani kaso na albashin ma’aikatan jihar Sokoto da gwamnatin ta yi domin bunkasa harkar ilmi shi ma ba gaskiya bane, kuma ba da amincewar ma’aikatan ake cire musu
kudin ba.
Haka kuma Lili ya kara da cewa kaf cikin garin Sokoto babu wasu ayyuka da Gwamna Tambuwal ya yi. Saboda ko cikin unguwar Mabera da ruwa ya malale babu wata gudummawa da Gwamna ya kai musu. Sannan kuma batun cewa Gwamna yana kashe milyan dari duk wata domin samar da ruwan sha a Sokoto ba gaskiya bane.
Ya ce makin da zai iya baiwa Gwamna Tambuwal shine na yawo a jirgi, inda ya kashe bilyoyin kudi, domin babu wani aiki da ya yi a ta kowane bangare da zai yaba masa. Kuma al’ummar Sokoto ba sune a gaban Tambuwal ba.
Lili ya kara da cewa a matsayin Tambuwal na wanda ya gagara jagorantar kananan hukumomi 23 dake Sokoto, ba zai iya shugabancin Nijeriya ba. Kuma duk ranar da Tambuwal ya fito neman takarar sugaban kasa, ba za mu mara masa baya ba. Domin idan muka mara masa baya mun ci amanar ‘yan Nijeriya.