Bello Hamza" />

Har Yanzu Sojojin Benezuela Suna Biyayya Ga Maduro

Shugaban sojojin kasar Benezuela ya sake jaddada goyon bayan su da shugaba Nicolas Maduro, biyo bayan kalaman da Shugaba Trump ya yi a kan kasar ta su.
Ministar tsaron kasar Benezuela, ya ce dakarun kasar za su ci gaba da zama a kan iyakokin kasar, kwana guda bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya ce, “za su iya amfani da kowanne irin zabi” domin ganin an samar da gwamnatin wucin gadi a kasar ta Benezuela.
A jiya Talata, ministan tsaron kasar, Bladimir Padrino, ya yi watsi da kalaman Trump a wani jawabi da ya yi ta talbijin, yana mai cewa, furucin shugaban “babu dattaku a cikinsa, sannan ba a taba yin irinsa ba.”
“Waye shugaban dakarun kasa da doka ta yarda da shi? Suna tunanin sune ke da kasar nan, kuma Donald Trump ya yi tunanin yana da karfin ikon da idan ya ba da umurni, dakarunmu za su bi?” inji shugaba Nicolas Maduro.
A ranar Litinin, yayin da yake jawabi a gaban ‘yan kasar Benezuela mazauna nan Amurka a jihar Florida, shugaba Trump, ya yi kira ga dakarun Benezuela, da su yi watsi da umurnin shugaba Maduro, su amince da tayin afuwa da shugaban wucin gadi Juan Guaido ya yi musu.

Exit mobile version