Har Yanzu Tsugune Ba Ta Kare Ba A Tsaron Jihar Katsina –Bincike

Tallafi

Daga Awwal Jibril ‘Yankara,

Har yandu dai tsugune ba ta kare ba a kan lamarin tsaro a jihar Katsina, musamman a Kananan Hukumomin Faskari, Sabuwa da Dandume, inda kusan kullum sai an samu labarin garuruwan da ‘yan bindida suka shiga suka kashe Mutane, ko Suka kwashe su domin neman kudin fansa, ko suka kore dabbobin da Suka mallaka.

Bincike sun nuna cewa garuruwa na baya-bayan nan da ‘yan bindigar Suka je, sun hada da Kauyan ‘Yar Daura da ke kusa da garin ‘Yankara, inda suka yi gaba da Mutum 11, dukkansu Mata, daga bisani suka nemi a ba su Naira Miliyan 10, bayan an cimma yarjejeniya, an biya su, kana suka sako su.

‘Yan bindigar sun je wasu garuruwan da suka hada da Unguwar Gizo, Unguwar Biri, Fankama, ‘Yar Itace, Tsuru, Mangorori, da sauransu, inda suka kore masu daruruwan shanu da tumakai, a wani garin ma har da kaji. ‘Yan bindigar sun kashe Mutane 10 a Unguwar Sarki, biyar a gidan Sarkin Makafi, Uku a Dankaya da wasu biyu a Jarkuka, duk a Karamar Hukumar Faskari.

Haka al’amarin yake a Karamar Hukumar Dandume da Sabuwa, inda ya zuwa yanzu kuma kusan duk wani kauye da ke cikin lungu sun fashe sun dawo garuruwan da ke bakin hanya don tsira da rayuwarsu.

A kwanaki biyu a jere, ‘yan bindigar sun kai hari a kauyukan ‘Yar Tasha, da Kwana Duke da ke Mazabar Tumburkai a Karamar Hukumar Dandume da kuma Doka da Garawa a Karamar Hukumar Giwa ta jihar Kaduna, inda Suka tafi da da mutane da dabbabo.Haka nan sun je kauyukan Dankaya, inda suka kashe Mutum uku, ciki har da jariri da Unguwar Hayaki a Mazabar Sheme ta Karamar Hukumar Faskari a Jihar Katsina.

Wannan na faruwa ne duk da dimbin jami’an tsaron da aka jibge a sansanin soja na Faskari, da ‘Yan Sandan kwantar da tarzoma da rundunar ‘Zaman Lafiya Dole’ ta Dan Zaki, yaran Marigayi Ali Kwara.

Exit mobile version