Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Har Yanzu ‘Yan Sanda Ba Su Gano Wanda Ya Ci Zarafin Ma’aikacin LASTMA

Published

on

Rundunar ‘yan sandar Jihar Legas ta ce har yanzu tana gudanar da bincike bisa zargin da ake yiwa jami’anta guda biyu wandan suka duki wani jami’in hukumar dake kula da hanya ta Jihar Legas. Kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar CSP Chike Oti shi ya bayyana hakan a ranar Asabar.

Majiyarmu ta labarta mana cewa a ranar Alhamis ne ‘yan sandar mobayal suka nadawa jami’in kashi a layin Ikorodu dake cikin unguwar Idiroko. Motarsa dai karan KIA ce mai lamba kamar haka GW 113 AAA, an ba da rahotan cewa ana zargin jami’in ‘yan sandar mobayal ne da rufe hanya.

An dai cafke ‘yan sandar mobayal din ne sakamako karya dokan hanya da suka yi. Ana zargin jami’an ‘yan sanda guda biyu ne da nadawa jami’in gwamnati duka a bainan jama’a tare da bata motar jami’in LASTMA.

Wani mai motan haya ya dauki bidiyan lamarin inda ya watsa a shafuffukan sada zumunta na zami. Mutane da yawa sun yi Allah wadai da hukuncin da jami’an suka dauka. Rundunar ‘yan sanda ta sha alwashin yin binciken lamarin tare da hukunta su idan aka same su da laifi. Kakakin rundunar ‘yan sandar Jihar Oti ya bayyana wa manema labarai cewa har yanzu suna gudanar da bincike aka lamarin.

Ya kara da cewa “muna kokarin yadda zamu gano su, jami’in da ya aikata wannan lamari dai baya cikin kayan ‘yan sanda, zai iya yiwa daga wani sashi yake na Jihar Legas. Amma zamu gano shi tare da wadanda suka aikita wannan mummunar aiki domin su fiskanci shari’a.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: