Connect with us

RAHOTANNI

Har Yanzun Muna Sauraron Tallafin Gwamnati – Alhaji Ibrahim Shehu Daudawa

Published

on

Sabon shugaban ‘yan kasuwar Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, Alhaji Ibrahim Shehu Daudawa, ya yi kira ga gwamnati da ta dubi halin da ‘yan kasuwan ke ciki ta tallafa masu. Shugaban ya yi wannan kiran ne sa’ailin da yake tattaunawa da manema labarai a ofishinsa da ke cikin babbar kasuwar ta Kaduna, a ranar Laraba.

Alhaji Ibrahim, ya bayyana cewa, irin tsarin da wannan gwamnatin ta zo da shi na tayar da koma dan tattalin arzikin ta, ‘yan kasuwan ne suka fi jin jiki da shi matu ka, domin da yawan ‘yan kasuwan shirin ya sabbaba masu rasa jarukan da ke hannun su. Wanda kuma wannan shi ne ya haifar da yanda kake ganin mutane masu yawa suna ta faman kasa kayayyakin su a bakin hanya da kuma kan titunan da suke kewaye da kasuwar. Domin rashin jarin ne ya sanya suka baro rumfunan na su da ke cikin kasuwa suka fito wajen kasuwar, domin ko dai jarin ya  kare ko kuma sabili da rashin cinikin a cikin kasuwar, in ji shi.

“Da wannan ne muke yin kira ga gwamnati, a duk lokacin da suka tashi saka ma ‘yan kasuwan kan irin ho b basa da fa di tashin da ‘yan kasuwan suka yi wajen kawo wannan gwamnatin, to ya kamata gwamnatin ta duba ta ga damuwan da ‘yan kasuwan suke da su ta kuma share masu hawaye. Babban damuwar ‘yan kasuwan kuwa a halin yanzun shi ne, suna neman samun tallafi daga gwamnati, ta yanda ‘yan kasuwan za su iya komawa gudanar da harkokin kasuwancin na su kamar da, wanda hakan ne zai sa ‘yan kasuwan su iya tsayuwa da dugadugansu suna kuma iya biyan ku da den haraji, wanda hakan kuma zai bun kasa tattalin arzikin Jiha da ma  kasa baki  daya.”

Daudawa ya ci gaba da cewa, “Mun san wannan gwamnatin ta zo da ayyuka masu yawa, ta  bangaren ilimi, lafiya, noma, tsaro, gine-ginen hanyoyi da makamantan hakan. Amma dai ta  bangaren kasuwa, to har yanzun dai muna sa rai ne, duk da muna da tabbacin Mai girma Gwamna zai cika al kawarin da ya yi na zai gyara harkar kasuwanci. Amma dai kawo yanzun mu ‘yan kasuwa ba mu shaidi wani tallafi ba daga wannan gwamnatin, muna nan dai muna ta baiwa gwamnatin goyon bayanmu kacokam.”

Shugaban ‘yan kasuwan ya bayar da misalin yadda aka tallafi manoma da kayan noma da sauran su, masu kiwon dabbobi har ma da na kaji duk gwamnatin ta taffa masu. “Don haka mu ma ‘yan kasuwa muna son gwamnatin ta tallafe mu da jari, wanda ko dai ba ruwa a cikin sa, ko kuma mai sau kin ruwan wanda za mu iya jalauta shi mu iya biya har mu sami namu a cikin sa.”

Kan kokawan da wasu ke yi na tsadan rumfunan babbar kasuwan ta Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, Alhaji Ibrahim Shehu Daudawa ya ce, duk wannan ana yi ne saboda rashin cinikin, “Domin matu kar kasuwa tana ja yadda ya kamata, to  dan kasuwa ba zai damu da ko nawa ne ku din rumfa ba, rashin cinikin ne ya kawo har wasu ke kokawa da hakan. In har a ce ana ciniki, tabbas a wata guda ma za ka iya mayar da ku din shagon da ka biya na shekara.

A  karshe, Alhaji Ibrahim Shehu Daudawa, ya kirayi ‘yan kasuwan da su  kara ha kuri, domin duk inda ka ga tsanani, tabbas sau ki ne ke biye da shi. Ya kuma bukaci ‘yan kasuwan da su ci gaba da yi wa gwamnati addu’i’o, da kuma ba ta goyon baya, domin gwamnatin tana sane da su, “Saboda in har ka  fara hango haske daga nesa, to tabbas yana nan tahowa ya same ka a duk inda kake,” in ji shi.

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: