Gwamnatin tarayya ta rasa kashi 42 na kudaden harajin da take samu a farkon wata ukun shekarar 2020, wanda ya sa aka rasa naira tiriliyan 1.29 a farkon wata ukun shekarar 2020. An dai samu kari fiye da na naira tiriliyan 1.25, wanda aka samu a farkon wata biyun shekarar 2020. Rahoton tattalin arziki na farkon wata ukun shekarar 2020, wanda Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana hakan. Ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta sama harajin naira biliyan 842.09 a farkon wata ukun shekarar 2020 na kashi 42.3 kasa da wanda aka yi tsammanin a kasafin kudi na naira tiriliyan 1.458. CBN ya daura alhakkin karancin samun harajin a kan matsalolin da cutar Korona ta haddasa ga tattalin arziki, wanda ya janyo gwamnatin tarayya ta rasa kashi 75 na kudaden haraji da ta ke samu.
CBN ya ce, “kudaden shigan da ake samu ya yi matukar raguwa a dai-dai lokacin da ake kara yawan kashe kudade wanda ya kai na naira tiriliyan 1.289.
“Wannan ne ya nuna an samu raguwar kashi 47.0 daga cikin kudaden da aka yi tsammanin samu a cikin kasafin kudi.
“Sakamakon raguwar samun kudade wanda aka yi tsammanin za a samu a cikin kasafin kudi ya samu ne saboda yadda gwamnati take ta kara kashi kudade a wajen dakile cutar Korona wacce ta haifar da matsaloli ga tattalin arziki, inda take kashi kudade ta hanyar gudanar da shirin bayar da tallafi da kuma rage kashe kudade a bangarn ayyukan more rayuwa.
“Wannan shi ne mafi munin raguwar haraji da gwamnatin tarayya ta ke fuskanta a kan hanyoyin samun kudaden shiga, wanda a baya ta yi tsammanin samun makudan kudade inda lamarin ya canza zani a halin yanzu.
“Gwamnatin tarayya ta kiyasta samun naira biliyan 508.14 daga wani asusun haraji na musamman, amma sakamakon cutar Korona wacce ta haddasa matsaloli ga tattalin arziki ya takaida samun kudaden ba kamar yadda gwamnatin tarayya ta yi tsammani ba.
“Sakamakon kudaden da gwamnatin tarayya tana tsammanin samu na naira tiriliyan 2.131 a farkon wata ukun shekarar 2020, ya yi karanci da kashi 21.1 bisa yadda aka yi wa kasafin kudin kwaskwarima.
“An dai rage kashi kudaden da ya kama a farkon wata ukun shekarar 2020 wanda ya kai na kashi 2.6 zuwa kashi 0.6, idan aka kwatanta shi da na shekarar 2019. Gaba daya dai an samu raguwar kashe kudade a shekarar wanda ya kai na kashi 45 daga cikin manyan ayyuka kamar yadda aka tsara a cikin kasafin kudi sakamakon raguwar haraji da aka samu.”