Rabiu Ali Indabawa" />

Harajin Gyaran Hanya A Kan Masu Sayen Mai Zai Tabbata…

 

Ga dukkan alamu kokarin da ake yi na tabbatar da masu sayen mai suna biyan wani kaso daga cikin kudin man da suke biya don kula da gyaran hanyoyin kasar nan ya kama hanyar tabbata, sa’ilin da gwamnonin kasar nan suka amince su yi hadin gwiwa da hukumomin gwamnati da abin ya shafa domin aiwatarwa.

An nunar da haka ne a cikin sanarwar da gwamnonin suka bayar bayan kammala taronsu a ranar Laraba da daddare.

Sanarwar wadda shugaban kungiyar gwamnonin, Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti ya rattaba wa hannu, ta yi bayanin cewa, gwamnonin sun amince su hada hannu da Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) da kuma Hukumar Kula da Kula da Gyaran Hanya ta Tarayya (FERMA) don tabbatar da aiwatar da harajin kashi 5 a cikin 100 daga cikin kudin da masu sayen mai suke biya da kuma harajin tashoshin motocin da ke jigila zuwa kasashen waje daga kasar nan, domin samar da kudin kula da gyaran hanyoyin kasar.

Har ila yau, kungiyar gwamnonin ta kuma gabatar da shawarar bunkasa ayyukan bankin ba da bashin gina gidaje don tallafa wa shirin samar da gidaje na gwamnati.

Gwamnonin sun kuma yanke shawarar hada kai da Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur, don tallafa wa aiwatar da shirin fadada iskar Gas na kasa (NGEP) ta hanyar karbar man gas na (LPG).

Sun kuma yi alkawarin samar da matakai don saukaka bututun iskar gas ta hanyar aikace-aikacen hanya da kuma karfafa kananan masana’antu, gami da horarwa ga masu aiki da iskar gas.

Sun ba da wannan shawarar ce a yayin taron kungiyar su karo na 12 a kan Korona wanda aka gudanar a ranar Laraba, inda karamin Ministan Ma’aikatar Man Fetur, Timipre Sylba ya gabatar da jawabi a kan NGEP.

Sun amince da aikin kwamitinsu a kan Korona wanda Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya jagoranta, kuma suka yanke shawarar yin aiki tare da Mataimakin Shugaban kasa  Farfesa Yemi Osinbajo a matsayinsa na shugaban kwamitin bunkasa dorewae tattalin arzikin kasa.

Sun bukaci gwamnatocin jihohi da su kara yin gwaji musamman don dakile yaduwar kwayar cutar ta Korona  tsakanin wadanda ke da yanayin da tsofaffi ke ciki dangane da hauhawar yaduwar cutar ta Korona tare da samar da saukinta ko kuma kawo karshenta da batar da alamarta.

NGF ta kuduri aniyar tallafa wa aikin kwamiti karkashin jagorancin gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta, da ya hada da aiwatar da matakan bude sassan tattalin arziki sannu a hankali.

A halin da ake ciki kuma, Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa akwai yiwuwar a sanya gwamnoni biyu a cikin kwamitin shirin tabbatar da dorewar bunkasa tattalin arziki da yake jagoranta.

Ya bayyana haka ne a yayin da yake shugabantar taron kwamitin ta shafin intanet a fadar shugaban kasa a jiya.

Sanarwar da mai taimaka wa mataimakin shugaban kasan bangaren yada labaru, Laolu Akande ya fitar, gwamnonin sun gabatar da bayani a gaban kwamitin a kan yadda jihohi za su yi hadin gwiwa da gwamnatin tarayya wajen aiwatar da shirin habaka tattalin arziki da aka ware wa Naira tiriliyan 2.3.

Sanarwar ta ce gwamnonin sun yi maraba da shirin da kuma yin aiki tare da kwamitin na gwamnatin tarayya, inda Osinbajo ya nunar da cewa yin hakan zai taimaka wurin yaukaka zumuncin aiki tare da gwamnonin.

Da yake wa manema labaru karin bayani, Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-rufai, wanda yake shugabantar kwamitin hadin gwiwa na kungiyar gwamnoni a kan aiwatar da shirin na habaka tattalin arziki, ya yaba wa kwamitin Osinbajo bisa namijin kokarin da kwamitin yake yi, kana ya ce gwamnoni sun dukufa sosai wajen tabbatar da nasarar shirin.

Ya ce kowace jiha za ta bayar da gudunmawar ekar noma 20 kuma gwamnoni za su ji daji sosai idan aka biya kudin tantancewa a matsayin tallafi. Haka nan ya ce gwamnoni suna murna da shirin gina gidaje 300,000 a sassan kasar nan inda ake san gina akalla 10,000 a kowace jiha.

Wakazalika, daga cikin abubuwan da aka gudanar a wurin taron har da gabatar da tsarin kashe kudin gwamnati a matsakaicin zango daga shekarar 2021 zuwa 2023 wanda Ministar Kudi Zainab Ahmed ta yi.

Wakazalika ta yi wa kwamitin bayanin kudin da ke cikin asusun gwamnati daban-daban da suka hada da asusun rarar man fetur da yake da Dala 72,406,952.48, asusun ko-ta-kwana Naira 40, 310,991,995.15 da kuma asusun bunkasa albarkatun kasa mai kunshe da Naira N131, 598,414,041.89, dukkan lissafin na ranar 7 ga watan Yulin 2020.

Exit mobile version