Sani Hamisu" />

Haramtacciyar Hanya: Kwastom Sun Kama Buhun Shinkafa 7,030 A Cikin Wata Daya

Jami’an Kwastom sun kama buhunhunan shinkafa guda 7,030, wadanda a ke shigowa da su ta haramtaciyar hanya a jihar Ogun, inda aka  yi amfani da motoci guda 38 kirar Takunbo, a tsakanin watan Mayu shekara ta 2019.

Mai kula da sashen yada labaran hukumar, Michael Agbara, shine ya bayyana hakan a ranar Talata a ofishin sa dake boda da Idiroko,wanda yake yankin karamar hukumar Ipokia na jihar Ogun.

Ya ce an kama buhunnan Shinkafan ne fiye da 7,000(50kg) a cikin watannin da suka gabata a shekara ta 2019.

Agbara ya ce kudaden kayan da aka kama wanda adadin su ya kai na Naira Miliyan Dubu tamanin da Miliyan dubu da Miliyan Dari da Miliyan dubu da Miliyan Dari da Takwas (165,105,105),kuma an samu kaya 411 na lantarki da kuma fetur 372.

“Wasu kuma mun samu sabbabin takalma guda 1,835,tare da motoci guda 264 da kuma buhunhunan sukari.”

Agbara ya ce ma’aikatan kwastam suna nan suna gudanar da ayyukan su kamar yadda doka ta tanadar, kuma suna yawan kai samame a cikin kogin Ipokia,Imeko Afon, Ilase, da Ihunbo da sauran guraren.

Agbara ya ce, “Dokar ta kara tsananta wajen kawar da duk wasu mutane masu shigo da kaya jihar Ogun ta gurfatatciyar hanya, domin kare mutuncin jihar Ogun.”

“An samu shinkafa fiye da 7,000 a watan Mayu 2019 shi ne mafi girma a kowane wata, saboda jami’an mu sun gudanar da aikin.

“Mun sami damar rage cin hanci da rashawa a jihar saboda ayyukan da Mike gudanar wa. Muna son mutane su sani cewa duk wani wanda yake safarar kayyayaki zuwa jihar Ogun ta haramtacciyar hanya to doka za tayi aiki akan sa.

“Bai kamata ace kasa kamar Najeriya ana shigo da kayayyaki cikin ta ba saboda kasar ce wacce take da arziki.Ta hanyar shigo da kayyayaki ana samar ma wasu mutane aikin yi a wajen kasar maimakon ya zama na ci gaban tana cikin kasar.”

Agbara ya yabawa jami’an Kwatan ganin yadda suke fadi tashi wajen ganin an dakile wannan arkallar, kuma ya kara da cewa zasu ci gaba da tafiyar da aikin su ta hanyar amfani da ilimi, da ma abubuwan da suka shafi zamantakewar al’ummar.

Exit mobile version