Connect with us

LABARAI

Haramtattun Bindiga Miliyan 10 Ke Hannun Jama’a A Afrika Ta Yamma -ECOWAS

Published

on

Kimanin kanana da matsakaitan haramtattun bindigogi milyan 10 ne suke boye a hannun jama’a a kasashen Afrika ta yamma, kamar yanda kungiyar kasashen na ECOWAS ta fada.

Shugaban kungiyar ta ECOWAS, Jean Claude Brou, ne ya fadi hakan jiya a Abuja, sa’ilin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a wajen babban taron kungiyoyi a kan yankin Sahel.

Jean Claude Brou, wanda Kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro na kungiyar ta ECOWAS, Francis Behanzin, ya wakilce shi, ya ce kimanin haramtattun makamai milyan 100 ne suke yawo a yankin na Afrika.

Ya ce, yawaitan bindigogi a yankin ne ke kara haifar da ta’addanci da sauran rigingimu a nahiyar ta yammacin Afrika da yankin Sahel.

“Rashin samar da wata dama ta ci gaba ga matasa da yanda yawan al’umma ke ta karuwa, duk su ke balbala wutar kafa haramtattun kungiyoyi da aikata laifuka,” in ji shi. Sai dai ya ce, kungiyar ta ECOWAS ta himmantu wajen warware duk wadannan matsalolin ta hanyar wasu shirye-shirye masu yawa da za ta yi a nahiyar.

“Dubarun da kungiyar ta tsara a yankin na Sahel sun kunshi wasu dubaru ne guda uku, (i) aiwatar da wasu manyan ayyuka da za su hada yankin, (ii) samar da abinci da kiyaye tsaron abincin, (iii) ilimi da manyan abubuwa: zaman lafiya da tsaro. Wannan yana tare ne da wani babban shiri da ya kunshi manyan ayyuka 31 wanda a jumlace an kiyasta za su ci dala bilyan 4.75,” in ji shi.

Wakilin babban Sakataren majalisar dinkin duniya a nahiyar yammacin Afrika da yankin Sahel, Mohammed Ibn Chambers ya ce, har yanzun matsalar tsaro a yankin na Sahel da tafkin Cadi abin tsoratarwa ne, kasantuwan yanda tashe-tashen hankula suka dabaibaye kasashe kamar su, Mali, Burkina Faso, Nijar da Nijeriya.

Ya ce, ECOWAS da majalisar dinkin duniya suna yin aiki tare da yankin na Sahel domin samar da zaman lafiya mai dorewa da ci gaba a yankin na Sahel.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: