Connect with us

LABARAI

Haramun Ne Saya Wa Buhari Fom Din Naira Miliyan 45 –Murray-Bruce

Published

on

Majalisar Dattijai ta bukaci Shugaban kasa ya mutumta dokar zabe da ta kayyade gudummawar da za a iya ba dan siyasa zuwa Naira Miliyan 1 kawai, majalisar ta kuma yi tir da saya wa shugaban kasar takardar tsayawa takarar shugabancin kasa a jam’iyyar APC a kan kudi naira Miliyan 45.

Mataimakin shugaban kwamitin watsa labarai da al’amurran yau da kullum, Sanata Ben Murray-Bruce, ya bayyaana haka a yayin da yake mayar da martani a kan saya wa shugaban kasa takardar tsayawa takara da wata kungiya ta yi, ya ce, ya kamata shugaban kasar ya bi ka’idojin dake tattare a cikin dokokin zabe ta kasa.

Murray-Bruce ya kuma kara da cewa, “Na farko Naira Miliyan 45 da jam’iyyar APC ke karba a matsayin kudin takardar takara ya yi matukar yawa, wanna kudade sun yi yawa ga duk wani ma’aikaci ko dan kasuwa mai neman na halas da yake bukatar tsayawa takara.

“Na biyu kuma in har wani mutum ya saya wa Buhari wannan Fom din, to yin haka ya karya dokar zabe saboda dokar ta ce ne, mutum ba zai iya karbar gudummawar da ta wuce Naira Miliyan 1 daga wani ba a matsayin gudummawa.

“A matsayinta na jam’iyya mai mulki ya kamata su bi dokokin da aka ayyana, in har Naira Miliyan 1 ne a ka ce, to ya kamata su bi doka, Naira Miliyan 45 da suka caza ya yi matukar yawa yawan kudaden ne ya sa ake naman hanyoyin karya doka, a halin yanzu jam’iyyar APC ce matsalarmu ba jam’iyyar PDP ba.”

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: