Connect with us

RAHOTON MUSAMMAN

Harbe-Harben Fadar Shugaban Kasa: Abinda Ya Faru Daki-daki

Published

on

  • Meye Ya Biyo Bayan Hatsaniyar?
  • Hakan Ya Nuna Gazawar Buhari Balo-balo, In Ji PDP
  • Me Shugaba Buhari Ya Yi Kan Lamarin?

 

Wani abin al’ajabi ya faru a fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, a daren Alhamis da ta gabata kan wani lamari da jami’an tsaro suka yiwa lakabi da ‘Sakaci’ ko ‘Wuce Gona Da Iri’ yayin da Dogarin matar Shugaban Kasa, Usman Shugaba yayi yunkurin tilas-tawa wani Sahibin Shugaba Muhammadu Buhari, Sabi’u Yusuf shiga kulle bisa tsoron ya dankwalo cutar sarkewar numfashi, wato ‘Korona’.

Wata majiya a fadar shugaban kasa ta shaidawa cewar, lamarin ya faru ne lokacin da Sabi’u, wanda dan-uwa ne ga shugaba Buhari ya koma gidansa dake farfajiyar fadar mulki, a Abuja ya na kofar shiga gidan, bayan dawowa  daga tafiyarsa zuwa Lagos, inda matarsa ta haifuwar jariri.

La’akari da ka’idojin Cutar Korona, kamar yadda wata majiya a fadar mulki ta labarta, Uwargida A’isha Buhari tare da ‘ya’yan ta guda uku, Zahra, Halima da Yusuf, hadi da wasu jami’an tsaro, karkashin jagorancin babban Dogarin A’isha, a daren ranar suka garzaya gidan na Sabi’u wanda ke daura da fadar mulki, inda suka bukace shi da ya shiga kulle na tsawon kwanaki 14 da zummar gujewa yaduwar cutar ta Korona ga iyalan shugaba da ma fadar gabadayanta.

Daga nan fa sai tarzoma ta barke tsakaninsu, inda shi Sabi’u Yusuf ya ke kalubalantar su da cewar, ai ba shine kadai mukarrabin shugaban kasa da ya ziyarci garin na Lagos ba, domin kamar yadda ya ce, sabon Hadimin shugaba, Farfesa Ibrahim Gambari yakan ziyarci garin na Lagos a kowane karshen sati, kafin ya tare da zama a birnin Tarayya, Abuja, don haka ya ke al’ajabin tilasta masa shiga kulle, saboda kawai ya ziyarci matar sa da ta haifu a Lagos.

Dogarin Buharin, Sabiu Yusuf, wanda ku kuma ake kiransa Tunde, lakabin da ake kiransa da shi bayan rasuwa mataimakin shugaba Buhari, Janar Tunde Idiagbon zamanin mulkin soji na shekarun 1980s, sai yayi burus da su ya shiga gida.

Shigarsa gida keda wuya, sai uwargidan shugaba tare da ‘ya’yan nata suka shiga fadin munanan kalamu, kamar yadda majiyar ta ce, lamarin da ya tilastawa Sabu’u arcewa da gudu, biyo bayan karar bindiga da Dogarin uwargida A’isha ya harba a iska, a yunkurinsa na kama shi wannan Hadimin Buhari, Sabi’u, wanda ya ketara ta Katanga, ya gudu zuwa masauki ko gidan Kawun Shugaba Buhari, Mamman Daura, inda ya kwana can domin tsira da ransa daga fargabar harbin da ya ji kararsu.

Madogararmu ta kuma labarto cewar, bayan da Babban Sufeton ‘Yan Sanda na Kasa, Mohammed Adamu ya samu rahoton wannan kwamacala da ya haddasa wasa da bindiga a farfajiyar mulki, wayewar garin Jummu’a, sai ya bayar da umarnin a cafke Dogarin Uwargida A’isha, hadi da jami’an tsaro dake tare da shi zuwa gidan Sabi’u Yusuf (Hadimin Buhari).

Umurnin kama wadannan jami’an tsaro, kamar yadda jaridar ta ruwaito,  ya biyo bayan jin labarin wasa da bindiga ne, wanda aka yi la’akari da cewar, kowane irin tashin-tashina ne, harbi da bindiga ya kasance wani laifi ne bisa dokoki ko sharuddan  tsaro musamman a cikin fadar shugaban kasar Nijeriya.

Lamarin dai ya fito fili ne, a daren na wannan Jummu’a lokacin da uwargidan shugaba tayi wa Babban Fifeton ‘Yan-Sanda Adamu umarni da ya saki Dogarin ta, daga tsare shi da aka yi.

Daga wallafinta da ta yi kan ya nar ta nagizo mai adireshin  @aishambuhari,  ranar Jummu’a da daddare, Uwargidan Shugaba ta rubuta cewar, “Koronabirus gaskiya ce, kuma babu shakka tana ta nan tana karade a cikin kasar mu Nijeriya.

Ta ce, “dangane da haka, ina mai yin kira ga dukkan hukumomin gwamnati sa suka dace, da su tilasta bibiyar dokar kulle, wacce Shugaban Kasa ya rattaba hannu, da karfafa yin hukunci da ita, da kuma aiwatar da bin ka’idojin hukumar yaki da cutattuka masu yaduwa (NCDC), musamman ma zirga-zirga tsakanin jiha da wata jiha. Duk wanda aka same shi da yin burus da wadannan ka’idoji, ya wajaba ya shiga kulle na tsawon kwanaki goma sha hudu, kuma ko shi wane ne, domin ba wanda ya fi karfi doka, wanda hakan masaniya ce wa rundunan ‘yan sanda.”

“Daga karshe, ina jaddada yin kira ga babban sufeton ‘Yan Sanda na Kasa da ya saki jami’in tsawo da aka wajabta mun, wanda har ga wannan lokaci da nake magana, su na tsare a hannun ’yan sanda, domin kare su daga shiga cikin wahala, ko yi masu shinge daga dankwalar cutar Korona, a yayin da ya ke tsare,”

Uwargidan Shugaba dai ba ta bayyana sunayen jami’an tsaron ta da aka tsare ba, kazalika ba ta zayya na dalilai ko lokacin da aka tsare su ba.

Majiyar ta fadar shugaban kasa, ta shaidawa jaridar cewar, biyo bayan rasuwar Mallam Abba Kyari, tsohon Hadimin Shugaban Kasa wanda cutar Korona ta zama ajalinsa, tun daga wancan lokaci, uwargidan shugaban kasa, take fadi-tashin ganin cewar, ta samu tasirin fadar mulki, illa dai tana da yakinin cewa wasu daga cikin ‘Yan-uwan mijin ta suna kokarin ganin ba ta cimma wannan buri nata ba.

Duk da haka, ta yi amfanin da wannan dama ta ziyara da Sabi’u ya kai zuwa Lagos ta rage masa tasiri, ta hanyar tilasta masa shiga kulle, da nufin cewar, hakan zai kare iyalanta daga daukar wannan cuta, da take hasashen Sabi’u ya dankwalo ko fargabar ya na dauke da cutar.

Jaridar ta kuma ruwaito cewar, Sabi’u ba shine Hadimin shugaban kasa daya kwal da bai tilastawa kansa shiga kulle ba, cikin wadanda suka kai ziyara wani gari daga fadar mulki ba.

Ana kuma da masaniya na cewar, biyu daga cikin ‘ya’yan shugaban kasa, Zahra da Halima, sun ziyarci surukunan su, lokacin da dan-uwan mijin Halima ya rasu a kwanakin baya, kuma basu shiga kulle ba bayan dawowar su zuwa fadar mulki ta Abuja, kamar yadda jaridar ta habarta.

LEADERSHIP A YAU ta nakalto cewar al’ummar Nijeriya sun bage da mamaki tun lokacin da wannan al’amarin ya faru, inda jama’a daga sassa daban-daban su ke ta bayyana mamakinsu da har aka yi sakaci matsalar ta fara kaiwa ga harbe-harbe.

Tun bayan faruwar lamarin babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya ta shaida cewar gazawar shugaban kasa Buhari ne ya kai ga jawo wannan mummunar aikin na kaito da takaici.

Kakakin jam’iyyar Kola Ologbondiyan shine ya shaida hakan ya mai cewa rashin tsari ne har ma ya kai ga hakan da kuma sakacin shugaban kasa Buhari kan lamarin tsaro.

To sai dai ya zuwa jiya, Fadar shugaban Nijeriya ta ce ana gudanar da bincike kan jami’an tsaron da suka yi harbe-harbe a kusa da gidan shugaban kasa da ke Aso Rock a Abuja.

A wata sanarwar da Malam Garba Shehu, mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari ya aike wa manema labarai ranar Lahadi ta tabatar da rahotannin da kafafen watsa labarai suka bayar cewa an yi rikici a fadar sakamakon hatsaniya da ta barke tsakanin mai dakin shugaban kasa Aisha Buhari da da wani mai taimakawa shugaban kasar Sabi’u Yusuf.

“Wannan lamari ya faru ne a wajen gidan shugaban kasa. An bai wa jami’an da ke dauke da makamai da na tsaro horo musamman kan yadda za su sarrafa makamai kuma idan suka gaza bin ka’idojin wannan horo, hukumomin da suka dauke su aiki suna da dokokin daukar mataki”.

“Shugaban kasa ya bi doka ta hanyar bai wa ‘yan sanda umarni a gudanar da bincike kan wannan abin taikaicin,” In ji Garba Shehu.

Duk da Garba ya shaida cewar shugaban kasa bai fuskantar wata barazana ta tsaro sakamakon faruwar hakan.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: