Harin Boko Haram: Gwamnatin Borno Ta Tabbatar Da Mutuwar Mutum 10

Daga Sulaiman Ibrahim

Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ziyarci asibitoci biyu a yau Laraba, bayan da mayakan Boko Haram suka harbo Rocket Propelled Grenades RPG, mutum 10 sun rasa rayukansu sannan 47 sun samu raunuka.

Harbe-harben, a ranar Talata da daddare, sun fito ne daga Kaleri, wani gari a gefen garin Maiduguri, zuwa garin Gwange da Adam kolo, dukkansu yankuna ne da ke da yawan jama’a a cikin garin.


Gwamna Zulum ya tabbatar da wadannan hare-hare a yayin ziyarar tausayawa da ya kai Asibitin Kwararru na Jihar, da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, duk a cikin garin na Maiduguri.

An shaida wa gwamnan cewa wasu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su sun samu raunuka daban-daban kuma ana ci gaba da kula da su, inda ya bayar da umarni ga ma’aikatar lafiya ta jihar da ta biya kudaden jinya.

Da yake magana kan sake dawo da Marte da sojoji suka yi, wanda ya fada karkashin ikon kungiyar Boko Haram kwanakin baya.
Zulum ya ce “Ina da kwarin gwiwa cewa maharan ba za su sake karbar Marte ba, ko wani yanki na garin Maiduguri”.

Exit mobile version