Connect with us

MANYAN LABARAI

Harin Boko Haram: Mutum 81 Sun Mutu, An Tafi Da Maigari Da Mutum Shida A Borno

Published

on

Wasu maharan da ake kyautata zaton Boko Haram ne sun kashe sama da mutane 81, a kauyen Foduma Kolomaiya, mai tazarar kilo mita 11 garin Gazaure da ke karamar hukumar Gubio a jihar Borno a ranar Talata.

Haka zalika kuma, shima garin Gubio yana da tazarar kilo mita 96 daga birnin Maiduguri na jihar Borno.

Wata majiya mai tushe ta bayyana yadda maharan su ka ci karen su babu babbaka a cikin harin, wanda su ka kai shi da tsakiyar rana, kafin a samu dauki.

Baya ga haka kuma, maharan sun kashe shanu sama da 300 tare da yin awon gaba da shanu 1000.

Har wala yau kuma, kasa ga awanni 24 wasu yan ta’adda sun kai hari a kauyukan babbar hanyar zuwa Monguno.

Jama’ar yankunan sun shaida wa wakilin, sun ce mutane da dama sun samu raunuka a cikin harin, wasu kuma sun yi batan-dabo bayan harin.

Duk kokarin jin ta bakin Daraktan yada labarai a rundunar sojojin Nijeriya, Mista Sagir Musa ta ci tura, amma wasu majiyoyin daya daga cikin kungiyoyin ayyukan jikai ta duniya a yankin arewa maso gabas, da shugaban daya daga kungiyoyin sa kai, a Gubio sun tabbatar da kai harin.

“Wannan harin yana daga cikin munanan hare-haren da aka kai a yan kwanakin nan,” in ji majiyar.

“Haka kuma, da wahala a iya gano wadanda da su ka yi batan-dabon, saboda yanayin kauyukan. An kashe mutane da yawa a wannan harin, sannan kuma wasu da yawa mun bata, saboda mummunan shirin da maharan su ka yi wa kauyukan, inda su ka zagaye yankin kana su ka yi ta harbin mutane.”

A nashi bangaren kuma, jami’in yan sintiri, ya ce ya kirga gawawakin mutum 69. Ya kara da cewa, “baya ga kuma wadanda su ka bace ba a San inda su ka shiga ba.”

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ziyarci kauyen Faduma Kolomdi, don ganewa idonsa ta’adin maharan Boko Haram su ka yi. Inda ya nuna matukar alhinin shi tare da jajantawa jama’ar garin.

Daya daga cikin mutanen da su ka tsallake rijiya da baya a harin ya shaida wa Gwamna Zulum cewa an kashe kimanin mutum 81 a harin, 13 kuma sun samu raunuka, sannan kuma maharan sun yi awon gaba da mutum 7, ciki har da mai garin kauyen.

Haka zalika kuma, Gwamna Zulum ya nemi sojojin Nijeriya su dauki ingantattun matakan dakile kashe-kashen, ta hanyar kawo karshen yan ta’addan Boko Haram, wadanda ke cin karen su babu babbaka a gabashin jihar.

Zulum ya fassara harin a matsayin aikin mugunta da keta tsantsar su. Wanda a tawagar sa ya dauko mutane biyar da su ka samu raunuka a harin, zuwa asibiti.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: