Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da harin da aka kai Cocin Ozubulu dake jihar Anambara a jiya Lahadi, ya kuma jajantawa shugabannin cocin da kuma gwamnatin jihar Anambara.
Shugaba Buhari ya kira Gwamnan jihar Anambara Willie Obiano ta waya inda ya jajanta masa akan harin, shugaban ya tabbatarwa da ‘yan Nijeriya cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kare lafiyarsu da dukiyoyin su a koda yaushe.