Rayuka Sama Da 29 Suka Salwanta
Sama da mutane 29 ne suka rasa rayukansu a wani sabon hari da aka ƙaddamar jiya a ƙauyen Nkiedonwhro da ke garin Irgwe na ƙaramar hukumar Bassa ta Jihar Filato. Mata da ƙananan yara ne wannan hari ya fi rutsawa da su.
Idan dai ba a manta ba, an samu wasu jerin hare-hare kwanakin baya a wasu ƙauyukan da ke ƙaramar hukumar, wanda hakan ta tilasta wa Gwamna Simon Lalong ayyana dokar ta ɓaci a yankin.
Duk da wannan dokar da gwamnatin Jihar ta sanya a ranar Juma’ar da ta gabata, an ci gaba da samun hare-hare, wanda ya sa jama’a suka fara yin hijira.
Sai dai Shugaban Cibiyar Irigwe, Sunday Abdu ya shaida wa majiyarmu cewa, waɗanda lamarin ya rutsa da su sun samu mafaka ne a wata makarantar Firamare da ke ƙauyen, wanda kuma Rundunar ‘Operation Safe Haɓen’ ne suka samar musu da mafakar.
A ta bakinsa, “Abin da ya faru tamkar wani shiri ne na share mu daga doron ƙasa, saboda an kawo farmakin da ya yi sanadin rayukan mutanen da basu ji ba, basu gani ba. Sojoji ne suka kwashe mutanen suka kai su wannan makarantar Firamare don basu mafaka bayan wani farmaki da aka kawo mana a makon da ya gabata. A nan ne aka zo a ka yi wa musu kisan gilla.
“Muna kan shirye-shiryen yi bizne su a kabarain bai-ɗaya. Mun samu tabbacin mutuwar mutane 27 waɗanda an ƙirga gawawwakinsu. Duk da wasu sun ce an samo gawar wasu ƙarin mutum biyu, amma wannan ba a kawo mana gawawwakin ba tukunna.” Inji shi
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ce, dole ne a daƙile wannan haukar domin maharani sun fara wuce gona da iri.
Kalaman na shugaban sun fito ne daga bakin mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya ce, tuni shugaban ƙasan ya umurci jami’an tsaro, waɗanda suka haɗa da sojoji, da ‘yan sanda da su tabbatar da sun kawo ƙarshen wannan aika-aika, tare da samar da hanyoyin hana afkuwar wani abu mai kama da hakan a nan gaba.
Ya ce: “Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari na iya ka ƙoƙarinsa wurin tabbatar da zaman lafiya, haɗin kan Nijeriya, kuma ya na kira ga dukkan al’ummun ƙasa da su zauna da juna cikin lumana da zaman lafiya.
“Ya na taya gwamnan Jihar Filato da al’umman jihar alhinin wannan lamari. Allah ya tausasa zukatan Iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.” In ji shi