Harin IPOB Kan Motocin Dakon Manja Ya Jawo Wa ‘Yan Kasuwar Galadima Dinnbin Asara – Mustapha Shu’aibu

Daga Ibrahim Muhammad Kano

kungiyar ‘yan kasuwar Galadima a Jihar Kano ta nuna rashin jin dadinta bisa irin take-taken da kungiyar IPOB ta Inyamurai ke yi da ka iya zama barazana ga zaman lafiyar kasa.

Shugaban kungiyar Kasuwar Alhaji Mustapha Shu’aibu shi ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da suka gudanar na nuna damuwarsu game da yadda IPOB suka kone musu motoci dauke da jarkokin Manja a Inugu.

Ya ce irin wannan barazana ya shafi hada-hadar da suke ta kayayyakin bukatun al’umma saboda ‘yan IPOB din su kan tare kayansu su lalata.

Ya ce ko a kwanan motocinsu makare da manja akan hanyarsu ta zuwa Kano daga Akwai Ibon ‘yan IPOB din sun far musu da harbi wanda hakan ya sa direbobi da sauran yaran mota suka tsallake domin tsira da rayukansu,yayin da ‘yan haramtacciyar kungiyar suka kone motocin guda biyu dauke da manja da hakan ya jawo musu asarar sama da Naira miiyan 80,000,000.

Ya ce wannan tasa wasu mutane da suka harzuka suka nemi fitowa su yi zanga-zanga a Kano. Amma saboda kar a yi abin da bai kamata ba a matsayinsu na shugabanni suka taushe su sannan suka hakura.

Ya ci gaba da cewa, yana kira ga masu ruwa da tsaki a Kano musamman gwamnatin jihar da ‘yan majalisun tarayya na kasa da Sanatoci kan lallai su tabbatar da Gwamnatin Jihar Inugu ta biya su diyyar asarar da aka jawo musu.

Ya kara da cewa rashin daukar mataki akan irin wannan zai iya jawo matsala domin duk lokacin da hakan ta faru suna kokarin su kare ‘yan kasuwar daga daukar doka a hannu. Idan kuma abin ya cigaba ba su san yanda za su yi da su ba.
Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar ta Galadima inda nan ne cibiya ta hada-hadar manja a Kano ya yi kira ga gwamnatin tarayya akan ta dauki mataki da ya dace domin kawo karshen irin wannan barazana da kungiyar IPOB take kawowa dan tabbatar da cigaban kasa da zaman lafiya.

Exit mobile version