Wani mazaunin yankin Kankara ya yi ikirarin cewa sace daliba 333 na Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati da ‘yan ta’adda suka yi a Jihar Katsina, ramuwar gayya ce ga harin da ’yan banga na garin suka kai wa Fulani. Da yake magana da Channels TB mutumin da ya yi furucin wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ’yan banga sun kai wa ‘yan fashin hari a cikin raminsu, sun kona gidajensu sannan kuma sun kashe wasu daga cikinsu.
Harin shi kansa martani ne ga wani hari da ‘yan banga suka kai a Kauyen’ Yar-Kuka, inda aka kashe wasu mutanen garin. Mazaunin ya ce: “Akwai abin da har yanzu mutane ba su sani ba; kafin sace daliban makarantar sakandaren Kankara na baya-bayan nan, ‘yan fashin a ranar Laraba sun far wa Kauyen ‘Yar-Kuka suka kashe mutane 12 tare da yin awon gaba da wasu mutane da ba a san adadinsu ba a kauyen.
Mazaunin ya ce, “a ranar Alhamis, kungiyar ‘yan banga sun hada kai suka bi bayan ‘yan bindigar a maboyarsu suka shiga kona gidajen Fulanin, suka ji wa wasu daga cikinsu rauni.” A cewarsa, ‘yan fashin sun tattara daliban a wani wuri suka dauke su zuwa kauyen Pauwa inda suka ajiye babura.
Satar ‘yan makarantar ya faru ne a ranar da Shugaba Muhammadu Buhari ya isa Daura, mahaifarsa don fara ziyarar sirri ta mako guda.