Zaman makokin na kwanaki 3 na zuwa ne a dai dai lokacin da adadin mutanen da tagwayen hare-haren kunar bakin waken da aka kai birnin Mogadishu ya haura mutum 200.
Gwamnatin Somaliya ta sanar da makokin kwanaki 3 bayan tagwayen hare-haren kunar bakin waken da aka kai birnin Mogadishu a jiya da ya hallaka akalla mutane 137.
A cewar shugaba Muhammad Abdullahi Muhammad Farmaajo za a fara makokin daga yau Lahadi don nuna alhini ga mutanen da suka rasa rayukansu.
Kawo yanzu akwai sama da mutane 250 da ke karbar kulawar gaggawa a asibitoci bayan samun munanan raunuka sanadiyyar harin na jiya.
Har ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta yi ikirarin kai harin.