Rahotanni daga jihar Anambra na cewa, a yau lahadi ne wasu ‘yan bindiga suka kai wani hari a wata coci (St Philips Catholic Church) garin AmaKwa Ozubulu a karamar hukumar Ekwusigo da ke jihar Anambra, inda akalla aka kashe mutum 15 yayin da aka jikkata 21.
Rahoton ya ce, bayan ‘yan bindigar sun shiga cocin sai suka fara harbi kan mai uwa da wabi, yayin da masu ibada kowa ya yi ta kansa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:45 na safe.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Garba Baba Umar ya tabbatar da aukuwar harin inda ya ce, yanzu haka hukumar tsaro na bincike akan kai harin.