Harin Ta’addanci Ya Hallaka Fararen Hula 36 A Burkina Faso

A Burkina Faso fararren hula akalla 36 suka gamu da ajalinsu sakamakon wani hari da aka kai musu a wasu kauyuka dake lardin Sanmatenga a arewacin kasar.

Wadanan kauyuka na daga cikin yankunan da suka dau niyar samar da yan banga domin yakar yan ta’ada.

A wannan hari,yan bindiga sun kona kasuwani dake yanki,yayinda Gwamnatin Burkina Faso ta sanar da daukar matakai  na baiwa matasan yankunan horo da makamai don kare kan su daga hare-haren yan bindiga.

Kasar Burkina Faso na daga cikin kasashen yankin Sahel dake fama da rashin tsaro musaman arewacin kasar duk da kokarin wasu kasashe kama daga Faransa da suka  aiko da sojojin su don yakar yan ta’ada a Sahel.

Exit mobile version