Harin ’Yan Bindiga A Zurmi: Dakta Dauda Ya Jajantawa Al’ummar Jihar Zamfara

Dan takarar Gwamnan Jihar Zamfara a karkashin inuwar Jam’iyyar APC, Dakta Dauda Lawal Dare ya mika sakon jaje ga al’ummar Jihar Zamfara bakidaya, musamman mutanen garin Gurbin Baure dake Karamar Hukumar Zurmi bisa ta’addancin da wasu ‘yan bindiga suka aiwatar a kansu.

Harin wanda aka kai shi da misalin karfe 9:00 na dare a Juma’ar makon da ta gabata, inda suka bude wuta akan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Dakta Dauda Lawal ya shaidawa LEADERSHIP A Yau alhininsa da wannan aikin ta’addanci, inda kuma ya yi addu’ar Allah Ya jikan wadanda suka rasa rai, Allah kuma ya ba iyalai da ‘yan uwansu hakurin wannan babban rashi.

Ya ci gaba da cewa, hakki ne da rataya a kan gwamnatin Jihar Zamfara na ta tabbatar da ta kiyaye rayuka da dukiyoyin al’umma.

“Ina mika sakon ta’aziyyata ga al’ummar Jihar Zamfara, musamman ma wadanda ke Karamar Hukumar Zurmi inda ‘yan bindiga suka aiwatar da ta’addanci a makon da ya gabata.

“Ina rokon Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu, Allah kuma Ya ba wadanda suka samu raunuka lafiya. Allah Ya kawo karshen wannan rashin imani a fadin Jihar Zamfara” Inji shi.

 

Exit mobile version